Shi'anci Da Shi'a



Ana amfani da wanna aure saboda nufinaure na shari'a da yaka iya hana kaiwa ga haram, da zina, ko istimna'i, ko amfani da wasu hanyoyi na haram domin kashe sha'awa, ga maras aure, ko kuma wanda ba ya iya hakura da mace daya, ko kuma ba zai iya aure ba sam, sakamakon kuncin rayuwa a lokaci guda kuma ba ya son fadawa cikin haram.

Ta kowane hali dai, halaccin auren mutu'aya dogara da littafi da Sunna ne, kuma sahabbai sun yi aiki da shi, da ya ksance zina ne da ba abin da wannan yake nufi sai cewa Allah da Manzo da sahabbai sun halatta zina wal'iyazu bilLah!.

Hada da cewa shafe shi bai zo dagalittafi da Sunna ba, kuma babu wani dalili a kan hakan.

Shi'a duk da sun halatta wannan aure bisadogaro da littafin Kur'ani da sunnar annabi sai dai sun fifita yin aure da'imi da tarbiyyar iyali domin samar da jama'a mai karfi, kada su karkata ga yin auren mutu'a haka nan duk da kuwa halal ne yinsa ga wanda ya so.

Haka nan Shi'a a bisa dogaro da littafinAllah da sunnar annabinsa da kuma koyi da wasiyyoyin imamai masu daraja (A.S) suna girmama mace matukar girmamawa, suna ba ta kima kwarai da gaske. Suna da hukunce-hukunce masu kayatarwa game da matsayin mace da hakkokinta da kuma mu'amala da ita musamman a fagagen kyawawan halaye da mallaka, da aure, da saki, da reno, da shayarwa, da ibada, da mu'amala, hukunce-hukunce masumuhimmanci a ruwayoyin imamansu da kuma fikihunsu.

27- Shi'a suna haramta: Zina, da luwadi,da riba, da kashe rai, da shan giya, da caca, da yaudara, da makirci, da algussu, da 'yar dubara, da boye kaya, da tauye ma'auni, da kwace, da sata, da ha'inci, da mugun nufi, da waka, da rawa, da kazafi, da tuhuma, da annamimanci, da fasadi, da cutar da mumini, da giba, da zagi, da alfahasha, da karya, da kire, da sauransu na manyan zunubai da kanana, kuma suna kokari matuka domin nisantar idan ake yinsu, suna kokari matuka domin hana su cikin al'umma ta hanyoyi daban-daban kamar rubutu da yada littattafai, da yin majalisosi, da hudubobi,da sauransu.

28- Shi'a suna himmantuwa da kyawawanhalaye, da son wa'azi, da jinsu, kuma suna shirya su a masallatai, da dakunantaro da gidaje, da filaye.

Kuma suna himmantuwa da addu'o'i da sukazo daga annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (A.S), kamar: addu'ar Kumail, da Abi Hamza, da simat, da jaushan, da makarimul akhlak, da iftitah, da ake yi a watan ramadan, kuma suna karanta su cikin nutsuwa da jin tsoron Allah, musamman tare da kuka da kaskan da kai, domin wannan yakan sanya tsarkake rayuka, da kusantazuwa ga Allah.

29 Shi'a suna himmantuwa da ziyarar kaburburanannabi da alayensa da zuriyarsa da aka binne a Bakiyya a madina mai haske, kamar kabarin imam Hasan Mujtaba, da imam Zainul Abidin, da imam Muhammad Bakir,da Imam Ja'afar Sadik (A.S).

A garin Najaf ma akwai kabarin imam Ali(A.S) da kuma garin karbala akwai na imam Husaini (A.S). Da na 'yan'uwansa, da na 'ya'yansa, da na 'ya'yan 'yan'uwansa, da na sahabbansa da suka yi shahada tare da shi a ranar ashura. A garin samra'u akwai kabarin Imam Ali Alhadi, da na imam Hasan askari (A.S). A garin kazimiyya kuwa akwai na imam Musa Kazim dana Imam Jawad, wadannan duka a garuruwan Iraki ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next