Shi'anci Da Shi'a



 Don haka ne Shi'a suke fadin wannan kalma domin ladan abinda ya zo a wannan ruwaya, amma ba domin tana wani bangare na kiran salla ba, domin idan wani ya fadi kalmar Ash'hadu anna aliyyan waliyyul Lah! a cikin kiran salla da nufin ita wani bangare ce ta kiran salla to ya zo da bidi'a, amma tunda ana fadarta ba da nufin ita wani bangare ce ta kiran salla ba, to ba bidi'a ba ce. Don haka, ba za a iya kiranta abin da ba shi da asali dagashari'a ba, kuma ba bidi'a ba ce.

24- Shi'a suna yin salla a kan turbaya ko fakon kasa ko kantabarmar kaba, ko wani dutse da dukkan abin da yake da asali daga kasa da tsurranta, banda shimfida da yadi da abin ci, da kayan ado, saboda ruwayoyimasu yawa da suka zo daga littattafan jama'a biyu cewa Manzo (S.A.W) ya kasance al'adarsa ita ce yin sujada a kan turbaya ko dandariyar kasa, kuma yana umartarmusulmi da hakan, don haka ne ma wata rana da Bilal ya yi salla a kan nadinrawaninsa domin gudun zafin rana mai kuna, sai Manzo (S.A.W) ya zo ya kawar da rawanin nasa daga goshinsa ya ce: Ka sanya goshinka a kasa Ya kai Bilal".

Kuma ya fada wa Suhaib, da Rabah, irin hakan yayin da yakecewa: Ka sanya fuskarka a turbaya ya Suhaib, Ka sanya fuskarka a turbaya ya Rabah (Duba Buhari, Kanzul Ummal, Almusannaf, da Assujudu alal ard na KashifulGida').

Ya zo a cikin littafin Buhari Manzo (S.A.W) Yana cewa: "An sanya mini kasa wajen sujada, kuma tsarki".

Kuma sujada a kan turbaya da dora goshi kan kasagun sujada shi ya fi dacewa ga sujada a gaban Allah (S.W.T) (S.A.W) domin shi ya fi sanyawa ga tsoron Allah kuma ya fi kusa da kaskan da da kai gareshi abin bautarsa (S.W.T). Kuma a lokaci guda yana tuna wa mutum da makomarsa da asalinsa. Shin ubangiji madaukaki bai ce: "Daga gareta ne muka halitta ku kuma a cikinta ne zamu mayar da ku, kuma daga gareta ne zamu futar da ku wani lokacin ba"?![11].

Ku sani sujada yana nuna matukar kaskantar dakai ne, da ba zai iya tabbata ba a kan shimfida da zani, da sauran kayan ado masu tsada. Tana iya tabbata ne da sanya mafi darajar waje a jikin mutum wato goshinsa a mafi kaskancin abu wato kasa. (Duba littafin alyawakit wal jawahir na sha'arani al'ansari almisiri daga malaman karni na goma).

Sai dai, ba makawa turbayar ta kasance maitsarki, shi ya sa Shi'a suke daukar wani guntu na turbaya, wanda yake an kwaba shi an mulmula shi domin su tabbatar da cewa suna sujada kan abu mai tsarki ne. Wani lokaci saudayawa kasar takan kasance an ciro ta ne daga wani waje mai tsarki kamar kasar karbala, wacce imam Husaini (A.S) jikan manzon Allah (S.A.W) ya yi shahada a cikinta, kamar yadda a wancan zamanin wasu sahabbai sun kasance suna daukar tsakuwowin kasar Makka domin su rika sujada a kanta a safararsu, domin neman albarka. (Duba littafin musannaf na San'ani).

Sai dai Shi'a ba su dage a kan haka ba, ba sulizimci hakan ba har abada, wani loaci suna sujada a kan kowa ce tsakuwa ce mai tsarki mai tsafta, kamar dakalin masallacin annabi da na masallacin ka'aba batare da wani kokwanto ba.

Kamar yadda ba sa sanya hannunsu na dama a kanhagu yayin salla, domin annabi (S.A.W) bai aikta hakan ba. Kuma wannan bai tabbata ba da nassi sahihi, shi ya sa ma malikiyya ba sa yin sa. (Duba Buhari, Muslim, sunan baihaki, da bidayatul mujtahidi na Ibn Rushdi al'kurdabialmaliki).

25-Shi'a suna yin alwala ta hanyar wankehannayensu daga gwiwar hannu zuwa 'yan yatsun hannu, kuma ba sa akasin hakan, domin sun dauki yadda ake yin alwala ne daga imamai jagororin Ahlul Baiti (A.S) wadanda su kuma sun koya daga manzon Allah ne (S.A.W) kuma su suka fi waninsu sanin me kakansu yake yi, kuma ya kasance yana yin haka ne. Kuma sun fassara kalmar "ila" da "tare da" ne[12], kamar yadda shafi'i assagirya kawo a littafinsa Nihayatul muhtaj.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next