Jagorancin Imam Sadik (a.s)



ZANGO NA BIYU:-

Zangon rike ragamar shugabanci. Wannan zangon ya dauki shekaru hudu da wata tara na halifancin Amirul Muminina Ali (a.s) da kuma wasu watanni na halifancin dansa Hassan (a.s). Duk da wahalhalu da matsaloli da damuwa da tsanani da yake tattare da wannan zangon, kamar yadda duk wata hukuma mai ra’ayin juyi take fuskanta, mafi haske da ban sha’awan shafuffukan tarihi ne suka kunshi bayanin aikace-aikacesa, kamar su mu’amala mai cikakkiyar dan Adamtaka da adalci da tsananin lizimtar hukunce-hukuncen musulunci ta fuskoki dabam-dabam wajen gudanar da al’ummar musulunci da kuma rikon magana daya da fayyacewa da jaruntaka wajen aiwatarwa da kuma daukan matsayi.


 

 

 

Wannan zango na tarihin imamanci ya zama abin koyi wanda Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka yi kira domin aiwatar da shi a rayuwar  siyasa da zamantakewa, tsawon karni biyu. Mabiya Ahlulbaiti suna kankame da son wancan yanki na tarihin musulunci, suna neman dawo da shi, suna kuma auna tsare-tsaren da suke rayuwa cikinsu da wancan zamani mai ban sha’awa. Da wannan ma’aunin  ne suke tuhumar tsare-tsaren da suka baude wa turbar musulunci. Mai ra’ayin sauyi a al’ummar wacce da bidi’a da baudiya suka addaba. Wannan halin da al’umma take cikinsa ya dorawa Imaman da suka biyo baya nauyi mai tsanani da mas’uliya  mai girma.

ZANGO NA UKU:-

Shi ne wanda ya dauki shekara ashirin,tsankanin sulhun Imam Hassan (a.s) a shekara ta 41 H zuwa shahadar Imam Hussain (a.s) a shekara ta 61 H.  Bayan sulhun Imam Hassan (a.s) an soma wani nau’in aiki mai kama da sirri wanda kuma manufarsa ita ce maido da jagorancin musulunci wa ma’abotansa na gaskiya tun da lamarin yana bukatar dako har sai mulkin Mu’awiya ya kare. Cikin wannan gajeran lokaci an fuskantar da kokarin kyautata  yanayi wajen yin shimfida ga zango na gaba.

ZANGO NA HUDU:-

A nan ya kamata mu yi bayani mai dan dama, tun da wannan zangon shi ya shafi laccarmu domin a ciki Imam Sadik (a.s) ya rayu. Cikin wannan zangon da ya dauki kusan karni biyu, tafiyar Imamanci ta ci gaba kan wani dogon layi domin canja al’umma har ta dace da ra’ayin musulunci a dukkanin fagage wadanda suka hada da jagorancin siyasa. Tafiyar sashe ta yi galaba sashe kuma ta gamu da ci baya; tana tattare da nasara mai girma a fagen tunani da akida, tana cudanye da salo daban daban na dabarun gudanar da kira, abin adonta kuwa shi ne ikhlasi da sadaukarwa da fana’i da girman dan adamtaka a idon musulunci, halayen da suka kai kololuwa da kuma matukar kyau.Wannan marhala ko zango ya fara daga watan Muharam shekara ta 61



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next