Jagorancin Imam Sadik (a.s)




 

 

 

 

 

Bayan Hisham ya gama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan bai ce ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa.  Yayin da mutanen nan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi  tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.

Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumaki wanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallaka na kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne? Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryi na farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sani cewa ) abin da aka jinkirtar  na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[21].

Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare  da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki. Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir ( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da  wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madina wanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sun kama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi.  Kada a ba su guzurin abinci ko ruwan sha.

Bayan kwana uku ana tafiya ba kakkautawa abinci da ruwan da yake tare  da su sai ya kare, a wani birni da ake kira Madin. Saboda umarnin Hisham, mutanen sun kulle kofifin birnin suka kuma ki sayarwa wadannan bayin Allah da komai. Yunwa  da kishi suka yi wa mabiya Imam tsanani. Sai Imam ya haura kan wani tudu wanda daga bisan shi ana iya hangar cikin birnin ya daga murya da kyau ya ce:-  “Ya ku mutan garin da mutanensa suka yi zalunci! Ni ne falalar Allah mai wanzuwa Allah yana cewa”:- Falalar Allah mai wanzuwa (bakiyyatul lahi ) ita ce mafi alheri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni ba mai tsaro ne a kanku ba”.

Mai riwaya ya ci gaba da cewa: Akwai wani tsoho tukuf a wannan birni, wanda ya ce da su: ‘Mutanena, wallahi wannan kira ne irin na Annabi Shu’aibu ( a.s). Na rantse da Allah idan ba ku fita kuka sayar wa wannan mutumin (abin da yake bukata) ba za’a kama ku daga birbishinku da kuma karkashinku. To lallai ku gaskata ni kuma ku bi maganta, domin ni mai nasiha ne a gare ku’.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next