Jagorancin Imam Sadik (a.s)



da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskata na kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Sai na juya ina kuka saboda abin da na gani. Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya  tafo har ya shigo dandali, ya kama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gare ni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn Yazid Alju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’. Da mutun  ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokin kara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya  ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[18]

Wannan misali ne na alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin  tsari sa alaka  kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna  sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[19]

Sannu a hankali bangaren fito-na fito  a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’a yana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).

            Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imam yake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar fama yana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya  kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Sai dai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa  yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa  a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba        maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.

A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yi kan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen  rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun  yi niyyar bincikar matsayin  Imam kan hukuma. Wannan ya sa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi an ce wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.

An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yi wa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumce kan Imam sannan jama’a su ci gaba.

 Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa: na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kuma na Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.

Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa suka saba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izinin zama  ba sai ya yi zamansa.

Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar  hasada da kufe  a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[20]Ya dai ci gaba da sukar sa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next