Jagorancin Imam Sadik (a.s)



((Bayan haka, Lallai Allah ya lamunce wa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[11]))   

A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s) yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasi na farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s). Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma.

Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasu an daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi  a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa. Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

RAYUWAR IMAM BAKIR (A.S)ZARCEWAR IRIN RAYUWAR IMAM SAJJAD.

An wayi gari mabiya Ahlulbaiti sun zama wata jama’a fitacciya mai dogaro da kai, kirar Ahlulbhaiti kuwa wacce ta dan tsaya ta kuma boye bayan shamaki mai kauri a dalilin waki’ar Karbala da waki’o’in da aka zubar da jini da suka biyo bayanta kamar waki’ar  Harra da tawayen Tawwabun  wadanda fir’aunancin Umayyawa ya haifar ta zama samamma ce mai yaduwa ta kuma bayyana cikin da yawa daga yankunan daular musulunci, musamman a Iraki da Hijaz da Kurasan. Tare da wannan samuwa, ta haifar da tsari na tunani da kuma aiki.       Kwanakin da Imam Sajjad (a.s) ya sifanta da cewa :  “ mabiyansa ba su wuce ashirin ba” sun kau sai ga Imam Bakir (a.s) yana shigo masallacin Ma’aiki (s.a.w.) a Madina jama’a mai yawa daga mutanen Kurasan da sauran lardunan duniyar musulmi suna kewaye shi, suna tambayarsa hukuncin musulunci kan al’amuran rayuwa dabam-dabam. Mutane kamarsu Dawus Yamani da Katada ibn Da’ama da Abu Hanifa da wadansu daga shugabannin mazhabobin fikihu suna tahowa domin su sha daga ilmin Imam ko kuma su yi jayayya da shi kan al’amura dabam-dabam.

 A wannan zamanin an sami mawaka masu kare mazhabin Ahlulbaiti da bayyana manufofinsa. Daga cikinsu akwai Kumait wanda ya sauwara mafi kyan surar da kwararru ke zaiyanawa a kan wilaya ta tunani da kauna ga mutanen gidan Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kasidarsa mai suna hashimiyya. Hakika harsuna basu gushe ba suna nakaltar wadannan gwalagwalan wake yayin da zukata suke kiyaye su.

Ta wata fuska kuwa halifofin Banu Marwana cikin wannan dan lokacin, sun sami wata natsuwa da tabbatar mulki bayan Abdulimalik ibn Marwan (m.86H) cikin shekara ashirin da ya yi mulki, ya murkushe dukkan masu ja da mulkinsu, kuma yiwuwa  cewa sansancewar aminci da natsuwa da halifofin Marwaniyawa na wannan lokacin ya samo asali ne daga kasancewar sun sami mulki tamkar wata ganima, sabanin magabatansu wadanda suka yi jan aiki kafin su kai ga mulki. Wannan natsuwa ta sa halifofin baya shagaltuwa da wasanni da jin dadin duniya, tadodin da galibi suke tare da mai jin iko da alfarma da kuma girma. Ko mene ne ma dai, damuwar halifofin Banu Marwan da lamarin mazhabin Ahlulbaiti ta ragu a wancan lokacin, sai ga Imam da mabiyansa suna rayuwa kusan a ce cikin aminci daga farautar hukuma. Bisa dabi’a, Imam zai ci tafiya mai yawa kan tafarkin tabbatar da manufofin mazhabin Ahlulbaiti a irin wannan yanayi ya kuma kai shi’anci wani sabon zango. Wannan kuwa shi ne ya bambanta rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta saura. Ana iya takaita abin da rayuwar Imam, cikin shekaru goma sha tara na imamancinsa (95-144H) ta kunsa kamar haka:-

Yayin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya zo cikawa ya yi wasici da cewa dansa Muhammadu ya zama Imami bayansa, gaba ga sauran ‘ya’yansa da danginsa, ya kuma ba shi wani akwati. Riwayoyi sun ce akwatin cike yake da ilmi, sun kuma ce akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a) a ciki. Imam Sajjad (a.s) ya ce:- “Ya kai Muhammadu wannana akwati ka tafi da shi gidanka” Sannan ya ce:- “Hakika babu dinari ko dirhami a ciki, sai dai cike yake da ilmi”[12]

La’alla wannan akwati wata alama ce mai muna cewa Imam Sajjad ya mikawa dansa  jagorancin tunani da ilmi (tunda yana cike da ilmi) ya kuma  mika masa nauyin jagorancin juyi (tun da yana kunshe da makamin Annabi (s.a.w.a)).

Gami da farawar Imam da mabiyansa faffadan aikinsu na yada koyarwar Ahlubaiti (a.s) farfajiyar yaduwar kiran ta kara fadi, ta sami sababbin fuskoki wadanda suka zarce fagenta daya gabata a Madina da Kufa. Sai ga ta tana yaduwa cikin  larduna manisanta daga cibiyar mulkin Umayyawa. Lardin Kurasan na daga cikin wadancan wurare kamar yanda riwayoyin tahiri suka nuna.[13]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next