Jagorancin Imam Sadik (a.s)




 

 

 

 

 

 

A nan za mu yi ishara ga kadan daga  wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamai yana daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yiwu mu sami bayani wannani al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.

Wannan abu ne wanda ba za’a iya gano shi ba. Abin da hankali zai kama shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan wannan lamari. Wannan  ita ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar  rashin  gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin  idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to  ya zama wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu da rabi, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).

Me ake nufi da tsari?  Ba fa tsari a nan yana nufin  wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba. Ba kuma samuwar wasu dakaru tararru masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba. Babu wannan, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayya kan wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.

Wannan  jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Ali na halifanci yana hada ta. Ta kan bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin ta da abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawa kan abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude. Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next