Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a, wanda ta jefa tsoro da firgici  a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya sa du mai da martani mai tsanani.

A takaice, a karnin farko da na biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadi na tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda  dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alwawiyyawa na musulunci. Wannan alaka ita ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.

Bisa hakika jama’ar shi’a  suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya.  Wannan shi ne takaitaceen  bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman  Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da  ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba! Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba  tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba.

Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.

Daga cikin kalmomi masu zufafan ma’anoni wadanda suke jan hankalin mai bincike mai bin diddigi a riwayoyin da rayuwar imamai (a.s) ko kuwa wadanda ake kawowa a maganganun masu  talifin karnin musulunci na farko akwai kalmomin “kofa” da “wakili” da “ma’a bocin sirri” wadannan kalmomi ne da ake  kiran wasu sahabban imami da su. Alal misalim mashaurin malamin hadisi dan shi’a yana fada dangane da rayuwar Imam Sajjad (a.s) cewa :- “ Yahya ibn Ummu Dawil shi ne kofarsa” a kan ta Imam Bakir ( a.s) kuwa ya ce: “Jabir ibn Yazid Alju’fi shi ne kofarsa”, batun rayuwar Imam Sadik (a.s) kuwa ya ce:-  “Muhammad Ibn Sinan shi ne kofarsa”. A cikin littafin “Rijalul Kashshi” ana kiran Zurara da Buraid da Muhammad ibn Muslim da Abu Basir da lakabin “ma’ajin sirri”. A cikin littafan hadisi ana ruwaito kalmar “wakili” daga Imam Sadik (a.s) a kan batun Mu’alla ibn Kunais. Ko wani daya daga cikin wadannan kalmomi imma dai ya fito ne daga Imam, wa imma sakamakon bincike ne mai yawa kan rayuwar imamai, wanda magabatan marubutan shi’a suka gudanar. Ko ma yaya ta kasance zabar wadannan kalmomi masu zurfafan ma’anoni ya samo asali ne daga wadansu fitattun alamomi a rayuwar Ahlulbaiti (a.s). Idan muka yi tunani da kyau kan wadannan kalmomi za mu tarar cewa ko wacce daga ciki tana nuni da cewa karkashin ayyukan zahiri wadanda imamayi (a.s) suke gudanarwa,  akwai wani rayayyen shiri na boye.

MA’AJIN SIRRI

            Idan mutum ba shi da wani “sirri” to ba shi da ma’ajin sirri. To mene ne wannan sirrin a rayuwar imamai? Me ne abin da sahabban imami a game ba za su iya rikewa ba sai wata jama’a da bata wuce a kidaya ta ba take da dacewa da cancantar rike shi? Kuma da haka ta sami darajar “ ma’ajin sirri”?

            Hankula na baya-bayan nan manisanta daga ainihin abubuwan da suka auku a tarihi da rarrabe su suna fassara wannan  sirrin da cewa shi ne sirrorin gaibi da iko kan ababen da suka keta al’ada da kuma mu’jizoji.

            Ni ina imani da ikon wannan sifa tsarkakka ta Ahlulbaiti wadanda Allah ya zabe su domin ci gaba da nauyin rungumar sako da iyar da shi bayan kaurar Manzon Allah, na yarda  suna dauke da irin wannan iko da irin da wadannan ilmomi. Kamar yanda nake imani da cewa adon da suka yi da wannan karfin da kuma wadannan ilmomi ko kadan ba ya karo da dubin da musulunci ke yiwa bil Adama da ka’idojin dabi’a da kuma dabi’ar kaunu. Amma fa wanna kari da ilmomi ba su ne “ sirrin imam” ba.  Ai irin wannan karfi da kuma ilmomi su ne mafi bayyanar dalilai mai tabbatar da imamanci da gaskiyar da’awar imani. To me zai sa imami ya boye wadannan al’amura ya kuma yi wasici ga sahabbansa da boyewa, a riwayoyi mayawaita, wadanda yawansu da karfafa juna ya kai littafan shi’a na hadisi suna kebe babi mai suna “babin boyewa”? Dole ne wannan sirri ya zama cewa idan ya yadu zai zame wa Imam da sahabbansa wani hadari mai girma, wannan kuma ba zai zama al’amuran gaibi da masu  keta al’ada ba.

            Shin sirrin shi ne ilmomi da ma’arifar Ahlubaiti? Shin shine irin ganinda mazhabin Ahlulbaiti yake yi wa musulunci da fikihunsa da kuma hukunce-hukunce sa? Ba mu musun cewa ilmomi Ahlulbaiti ana yada su a zamanin danniyar Umayyawa da Abbasiyawa ta hanyar hikima da dabara domin kada ko wani sususu da shashasha ya kutsa cikinsu, amma wadannan ilmomi ba zai yiwu a ce su ne sirrin Imam ba. Duk da kebantar da take tattare da wadannan ilmomin ana karantar su a daruruwan makarantin  fikihu da hadisi a wadansu manyan biranen lardunan musulunci a wancan lokacin. ‘Yan shi’a sun kasance suna nakalta wa juna wadannan ilmomin tare da sharhinsu. Muna iya cewa wadannan ilmomi da ma’arifa kebantattu ne amma ba na sirri ba. Kebantuwarsu tana nufin cewa yaduwarsu ta takaita ga haular ‘yan shi’a, amma a halaye na musamma suna isa ga wadanda ba shi’a ba ma. Sam ba masu takaita da kadan daga sahabban  imamai, boyayyu ga wanin su ba ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next