Jagorancin Imam Sadik (a.s)



“ Alhamdu lillahi an dauke hanin. Muna nan muna sauraronka a ranar da muka ajiye”.

Sidi ya yi iya kokarinsa domin a karbi uzurinsa amma ina Sheikh Mufattih bai gamsu ba, sai ya amsa da cewa:- “Mun riga da mun sanar da batun laccan nan cikin jami’o’ i” Sidi ya ba da dalilin cewa samun tikitin  jirgi yana da wahala. Amma Sheikh sai ya ce a shirye yake ya saya masa tikitin, saboda haka ba makawa ga halartar  Sidi!

A ranar laccar ya baro Mashhad ya kuma iso Tehran yan sa’ o’ i kafin lokacin  farawa, sai ya wuce zuwa masallacin kai tsaye. Yayin da mai masaukinsa ya gan shi, ya yi farin ciki matuka, a lokacin kuwa yana tare da matasa kamar dari  biyu suna  jiran a ta da salla. Ana cikin salla matasa sai zuwa suke yi har adadinsu ya kai dururuwa da dama. Bayan’yan mintoci sai ga dalibai gungu gungu  suna ta shigowa, wannan bayan an tashi daga darasi a jami ‘o’ i kenan.

Masallacin da farfajiyarsa da loko-lokon da ke daura dashi duk suka cika makil  da mutane. Sidi ya fara lacca yana rike da takardu guda arba’in wadanda suke kunshe da muhimman batutuwa kan laccar. Ya ci gaba da bayani wanda ya dauki hankalin masu  sauraro, kai ka ce tsuntsaye ke bisa kawukansu saboda tsananin natsuwa. Laccar ta dauki tsawon sa’a uku amma sashen  takardun  nan kawai Sidi ya sami damar sharhinsu. Da ya zo rufewa sai ya daga wadancan takardu arba’in yana mai ishara da cewa lokaci bai ba shi damar gabatar da dukkanin abin da ya yi niyya ba.

Bayan wannan zama ba a dade ba sai aka kama Sheikh Mufattih aka hana shi salla a masallacin Javid. Bayan an sako shi sai ya koma masallacin Kuba. A nan, ya zama wajibi mu yi nuni da wani muhimmin al’amari, shi ne :  Sidi Khamene’i (Allah ya kiyaye shi ) ya gabatar da laccan  nan ne shekara ashirin da suka wuce. Kuma babu shakka ya yi nazari da bincike mai yawa kan rayuwar Imaman Ahlulbaiti (a.s) saboda haka ta yiwu yana da wadansu sababbin ra’ayoyi ko kuma ya canja ra’ayi, kan wata mas’ala daga cikin mas’alolin da ya gabatar cikin jawabin. Hakika mun so mu san ra’ayinsa kan wadannan mas’aloli domin mu cimma ra’ayoyinsa na baya-bayan nan kafin mu soma tarjamar wannan jawabin zuwa harshen  larabci. Amma nauye-nauye da tarin ayyuka da cushewarsu ya hana hakan. Saboda haka za mu gabatar da ita kamar yanda take. A cikinta akwai sabon ilmi mai yawa da kuma gadon tunane-tunanen musulunci kamar yanda ake tattauna shi a Iran gabanin nasarar Juyin Islama, abubuwanda suke da muhinmanci ga duk wani mai bincike.

Ana iya lura da cewa Sidi ya yi fito-na-fito da ra’ayoyi guda biyu wadanda yake yawan sukar su a laccocinsa da darussansa. Wadannan kuwa su ne: Ra’ayin gurguzu mai sukan musulunci da alamominsa, yana sifanta mazajen musulunci  da cewa ba su tabuka komai ba wajen kare hakkin matalauta da wadanda aka zalunta, dadin dadawa ma sun kasance madogarar azzalumai da masu hanu da shuni! Na biyunsu shi ne ra’ayin wanda suka yarda an rinjaye su. Saboda rinjayarsu da aka  yi sai suka kasance ba su da katabus, kokari suke su sami abin da wai zai zame musu hujjar rashin motsawa, a cikin tarihin rayuwar Imaman musulunci. Wadannan ra’ayoyi sun yi tasiri a kasar Iran kafin habakar Juyin Islama, sun kuma zamo karfen kafa ga masu kiran al’umma zuwa hanyar musulunci.

Dokta Muhammad Ali Azarshab.

Da sunan Allah, mai rahama mai jin kai.

(Daga muminai  akwai wandansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah Alkawari a kansa, sa’annan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukatarsa, kuma basu musanya ba, musanyawa) –Ahzab 23

(Kuma muka sanya su shugabanni suna shiryarwa da umurninmu. Kuma muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alheri da tsayar da sallah da bayar da zakka. Kuma sun kasance masu bauta garemu).-Anbiya 73.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next