Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Alminhal bin Umar ya ruwaito cewa:-  “Na kasance ina zaune tare da Muhammad bn Ali Albakir  (a.s) sai wani mutum ya taho ya ce da shi: Yaya kuke?  Sai Imam Bakir(a.s) ya ce:- “Lokaci bai yi  ba da za ku  san yanda muke?  Misalinmu a wannan al’umma tamkar Bani Isr’a’ila ne a da,ana yanka ‘ya‘ya maza ana barin (raya )mata.  Ka saurara!  Lallai wadannan suna yanka ‘ya‘yanmu maza suna barin  ‘ya ‘yanmu mata. Larabawa sun yi da’awar  fifiko bisa baibayi. Sai baibayin suka ce: ‘Mene ne dalilin haka?’  Sai suka ce:  “Muhammadu balarare ne daga gare mu” Sai suka ce da su:  “Kun yi gaskiya.” Kuraishawa kuwa suka yi da’awar cewa suna da wani fifiko bisa sauran larabawa. Sai sauran larabawa  suka ce “Mene ne dalili?” Sai suka amsa da cewa:  ‘Muhammadu bakuraishe ne’. Suka ce da su: ‘Kun yi gaskiya’. Idan mutanen nan sun yi gaskiya, to muna da fifiko bisa mutane domin mu zuriyar Muhammadu ne, mutanen gidansa kuma makusantansa masu kebanta da shi, waninmu ba ya tarayya da mu a wannan” Sai mutumin ya ce da Imam;  “Wallahi ni ina son ku, ku Ahlulbait”. Sai ya ce da shi: “To ka dauki bala’i a matsayin riga, domin kuwa wallahi shi (bala’i) ya fi kusa da mu da kuma shi’armu bisa ga gudanar igiyar ruwa a cikin kwari. Da mu bala’i zai fara sanan  ku”[17]

Da ganin alamar cewa mutumin ya girgiza saboda zaburarwar da ya ji sai Imam ya yi maza ya zana  masa tafarkin kiran, ya fayyace.Shi dai tafarki ne wanda  aka shimfida shi da jini da kwalla, Imam kuwa shi ne madugun tafiyar, bala’i yana samunsa da farko  kafin ya kai ga shia’rsa.

A tsakanin shi’arsa alakar Imam tana da wadansu sifofi kebantattu. Za ka gan shi cikin mabiyansa tamkar yanda kwakwalwa take a tsakanin gabban jiki yana ciyar da ruhinsu yana karfafa masu haraka  da himma ba tare da yankewa ba.

Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai ba wa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.

Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da Imam Bakir(a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma  yi fita irin  ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar  da darasin rike sirri ga wannan  sabon dalibi  wanda ya ga alamun  iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai ya zama ma’abocin sirrin Imam.

  Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir ya ce:-

“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fito yana farin ciki. (Muka kama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a. Muka yi salla. Mun kama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya ta kan idanunsa. Sai ga shi a rubuce(( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai ya ce da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin ya ce: ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai ya ce : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya ci gaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.

Numan ya ci gaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka:

‘Na san Mansur mutumin mutane;

Mai umurni ba’a umurtansa’



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next