Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Wata mas’alar da ba makawa ga karfafawa game da ita a wannan bayanin ita ce, a wadansu lokutan Imam Sadik (a.s) ba ya takaita kan tabbatar da imamancinsa kadai, yana ma ambaton sunayen imaman gaskiya magabatansa tare da ambaton nasa sunan, watau, bisa hakika, yana gabatar da silsilar imaman Ahlulbaiti tare da sadarwa, daya bayan daya, ta yanda yayyankewa ko rarrabewa ba ya yiwu wa.

Wannna matsayin yana nuni da dangantakar da ke akwai tsakanin jihadin imaman Ahlulbaiti (a.s) da dorewarsa tun daga zamunnan da suka gabata har zuwa lokacin Imam Sadik (a.s). Imam Sadik (a.s) yana bada sanarwar imamancinsa a matsayin shi na wani sakamakon  da ba makawa zai biyo bayan imamancin magabatansa, kuma da wannan yake bayyana tushen wanna kiran da zurfin kafuwarta  a tarihin sakon musulunci, da dangantakarta da ma’abocin kiran, Manzon mai girma, mafificin tsira da aminci ya tabbata gare shi. Bari mu kawo wasu samfurin kiran Imam:-

Riwayar Amru ibn Abi Mikdam ita ce  mafi ban-sha’awa a wannan babin, tana kuma sauwara wani yanayi mai ban mamaki.

A ranar tara ga watan Zulhijja, yayin da mahajjata suka taru a Arfa domin tsayuwa gashi sun riga sun hallara a wannan wuri daga ko ina: kamar daga karshen kasar Kurasan har zuwa gabar tekun Atlantika,  a wannan wuri mai hadarin gaske, inda kira a cikinsa tana iya aika amon ta zuwa nisan duniyar musulunci. Imam ya hadu da wannan taron jama’u masu yawa saboda ya isar musu da kalmarsa. Mai ruwaya yace:- na ga Imam ya tsaya cikin jama’an nan, ya daga murya da kyau domin ya isa kunnuwar mahalarta sannan daga bisani ya kai ga kunnuwan  talikai, yana kira kamar haka:-“Ya ku mutane ! Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne shugaba (imam), sannan Ali ibn Abi Talib, sannan Hassan, sannan Hussaini, sannan Ali ibn Hussain, sannan Muhammad Ibn Ali, sannan ……..” Yana wannan kiran sau uku ga wadanda suke gabansa, da gefensa na dama, da gefensa na hagu da kuma bayansa, kira goma-sha biyu ke nan”[33]

A wata riwayar daga Abu Sabah Alkinani cewa Imam Sadik (a.s) ya sifanta kansa da kuma imaman shi’a da cewa ganima (anfal) da zababben dukiya tasu ce.

Daga Abi Sabah ya ce:- Abu Abdillah ( a.s) ya ce da ni: “Ya Aba Sabah, mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu. Ganima tamu ce, zababben dukiya namu ne, mu ne matabbata cikin sani kuma mu ne wadanda aka yi wa hasada wadannan da Allah ya fade su cikin littafinsa”[34]

 Safwul mali, zababbar dukiya, shi ne kayayyakin da suke da kima matuka daga cikin ganimar yaki. Da ba’a raba wa mayaka irin wadannan kayayyakin kamar yanda ake raba musu sauran dukiyar ganima saboda kada a fifita wani da  zababben abu, gudun kada wannan ya zamewa wani wata daraja ta karya. Maimakon haka ana barin irin wadannan kayayyaki ne a hannun shugaban musulunci ya yi amfani da su wajen abin da zai tabbabtar da maslahar musulmi gaba daya. Azzaluman mahukunta su kan dauki irin wannan dukiya su kebanta da ita ta hanyar kwace(gasabi). Imam yana fayyacewa kan cewa  zababbar dukiya, wajibi ta zama tasu, haka nan ganima. Wannan yana nufin cewa Imam yana bayyana kansa a sarari a matsayin shugaban musulmi a ganin shari’a, wanda nauyin jujjuya wadannan dukiyoyi dai-dai da abin da yake ganin zai tabbatar da maslahar al’umma  a kansa yake.

A wani hadisin Imam Sadik (a.s) yana ambaton sunayen imamai magabatansa daya bayan daya, yana ba da shaidar imamancinsu da wajib cin biyayya gare su. Yayin da ya iso kan sunansa sai ya yi shiru, masu saurare kuma sun sani sarai cewa gadon ilmi da hikima bayan Imam Bakir (a.s) a wajen Imam Sadik (a.s) yake.  Kuma da wannan Imam (a.s) yake bayyan hakkinsa na jagorantar al’umma, yana bayyana  shi da wani salo mai danganta hakkin nasa da kakansa Ali ibn Abi Talib (a.s). Cikin wadansu babi-babi na littafin Alhujja cikin Alkafi da ma cikin juz’i na arba’in da bakwai na Biharul Anwar akwai irin wadannan hadisai da yawa, suna fayyacewa, wani zubin kuwa suna kinaya kan da’awar imamanci da kuma kira gare ta.

Domin tabbatar da wannan batu na tarihi, akwai hujjoji ko shaidu da suke tabbatar da samuwar wani tsararren shirin sadarwa da yake gudanar da kiran Imam (a.s) a ko ina cikin sassan duniyar musulunci. Mayawaitan hujjoji da ke akwai a kan wannan batu sun sa samuwar wannan shirin sadarwa wani al’amari ne yankakke ba wani shakka a kansa. Wadannan shaidun sun yi yawa da karfin da ana iya kafa hujja da su a kan wannan maudu’i namu, hujja tabbatatta, ko da ba’a sami sahihin  hadisi ko guda ba kan wannan batu.

Mu dubi  wadannan tabbatattun al’amuran tarihin:-



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next