Jagorancin Imam Sadik (a.s)



            Gaskiyan al’amarin shi ne sirrorin su ne al’amuran da suke ta’allaka da bayanan da suka danganci shirin tsare-tsaren imami,……….shirin da yake kutsawa cikin filin daga a siyasance da zimmar cimma manufar juyi,…… ko wadanda suka danganci dabarun da shirin ya haifar, ko ayyukan da zai aiwatar, ko suka danganci sunaye da nauye-nauye mambobin shirin ko hanyoyin kudi ko labarai, da rahotannin da suka ta’allaka da muhimman ababen da suke faruwa. Wadannan da ire-irensu sirrori ne wadanda ba dama wani ya tsinkaya idan ba jagora ba ko mataimakan da suke rike da ayyuka daban daban. Tana yiwuwa a sami yanayin da ya dace da bayyana wadannan sirrori a kwaye lulubinsu, ko a kusa ko kuwa tare da jinkiri, sai dai kafin wannan lokaci ba dama wani ya sami masaniya kan wadannan sirrori face wanda aikinsu yake da dangantaka da su kai tsaye, su ne kuwa “ma’ajin sirri”. Duk wani zarcewarsu zuwa ga makiya (shi kuwa laifi ne mai girma wanda ba’a yafewa) laifi ne wanda ka iya janyo rushewar jihadi da ayyuka da kuma tsararrar jama’an nan. Wannan zai fahimtar da mu abin da Imam (a.s) yake nufi da cewa:  “ Jidalin da mai gaba da mu (nasib) yake janyo mana baya wuce wanda  mai baza sirrinmu zuwa wanda ba ahalinsa ba yake jawowa. Mai baza sirrinmu  ba zai bar duniya ba sai makami ya ci shi”[48]

KOFA DA WAKILI

A  alakar sirri tsakanin Imam (a.s) da shi’a ta yiwu a bukaci isar musu da wasu bayanai ta hanyar “ mai shiga tsakanin” ko kuma sila. Wannan kuwa dabara ce mai ma’ana, abin da aka saba bisa alada. Yan leken asiri masu lababawa da zimmar gane alakokin Imam (a.s) su kan faki zaman ganawarsa da mabiyansa a lokacin aikin haji a Makka da Madina yayin da ayarai daga nisan duniya suke zuwa. Fakon wadannan zama ya kan kai ga ganowa bakin zaren babban shirin tsare-tsaren Imam. Saboda haka kake ganin Imam (a.s) wani lokaci yana nisanta wasu mutane daga gare shi da kalami mai taushi, a wani lokacin kuma da lafazin suka. Alal misali Imam ya ce da Sufyan Sauri:- “Kai mutum ne abin nema, sarauta kuma tana da ‘yan leken asiri a kanmu, saboda haka ka fita amma ba korar ka aka yi ba”[49]

Wani lokaci sai ka ga Imam (a.s) yana rokon jinkai ga mutumin da ya yi kicibis da shi a kan hanya amma ya kau da kai kamar bai gan shi ba, a  wani zubin kuwa yana laifanta wani wanda ya gan shi a makamancin wancan yanayin ya kuma yi wa Imam sallama tare da karramawa da girmamawa.[50]

            Irin  wadannan yanayi na bukatar samuwar wani mutum da zai zama sila taskanin Imam  da mai neman bayanai masu iso shi daga wajen Imam, to wanna silan shi ne “kofa” kuma wajibi ne ya zama daya daga mafiya amincin mabiyan Imam, wadanda suka fi kusaci da shi, kuma suka fi wadatuwa wajen sanin bayanai da hanyoyin sadarwa. Dole ne ya zama tamkar kudan zuma wacce da muggan kwari za su san zumar da take dauke da ita da sun sassare ta sun kuma kai hari kan gidanta.[51]

             Ba banza ba muke ganin wadannan “kofofi” galibi ana farautarsu ana kamawa ana dira kansu da mafi munin nau’in azaba.

            Yahya ibn Ummi Dawil, “Kofar” Imam Sajjad an kashe shi, mummunan kisa.[52]  Jabir ibn Yazid Alju’fi kuwa dole ta sa ya sa rigar hauka kuma wannan labarin ya watsu ya zama dalilin tsirarsa daga kisan da halifa ya riga da ya bayar da umurninsa ‘yan kwanaki kadan kafin yaduwar labarin haukacewarsa. Muhammad ibn Sinan kuwa ‘kofar’ Imam Sadik (a.s) korarsa  Imam ya yi, kora ta zahiri duk cewa Imam ya bayyana yardarsa gare shi da yabonsa a wasu wuraren. Ba don komai aka yi masa haka ba sai domin shigarsa irin wadannan hadura, kamar yanda sanarwar Imam  cewa ba shi da wani sananne  mashahurin marawaici wanda kuwa ya rabauta da sanarwar yarda daga Imam. Sau da dama yana ishara, bisa ra’ayi mai karfi, cewa dabara ce ta tsare-tsare.

            Irin wannan makoma tana fuskantar “wakili” shi ma. “Wakili” shi ne mai nauyin tara dukiyoyin da suke da alaka da Imam da kuma rarraba su. Shi ma ya san sirrori masu yawa, alal akalla, sunayen masu bayar wa da na masu karba. Wadannan bayanan, makiya Imam basu raina su. Mafificin hujja kan haka shi ne makomar Mu’alla ibn Kunais, wakilin Imam Sadik (a.s) a Madina da kalmomin Imam game da Mufaddal ibn Umar, wakilinsa a kufa, wadanda ya fade su bisa takiyya.

Lakabin nan guda uku: kofa da wakili da ma’abocin sirri, wadanda muke samun cewa masu su wadansu wanyan mutane ne daga mazajen shi’a suna bayar da haske kan halin da shi’a ke ciki da alkarsu da Imam da kuma harakar tsare-tsare ta shi’a.

Da wannan dubi muna iya fahimtar cewa shi’a su ne jama’ar mutane masu sajewa da junansu, jama’a mai manufa, mai himma, mai matattara a kan wani ginshiki mai tsarki wanda yake watsa haske kan mataimakan sa ta hanyar umurce-umurce da shiriyarwarsa. Su kuma mataimakan suna da alaka da shi, suna kawo masa bayanai, suna kame motsin rai suna kuma fin kafin zuciyarsu albarkacin wasice-wasicensa na hikima. Suna kuma lizimtar salon sirri wajen aiki, kamar kiyaye sirrori da karancin magana da rashin shiga mutane da aikace –aikacen jama’a da kuma nisantar al’amuran kawo juyi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next