Gudummawar Mace



"Ya kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a gare ka a kan ba za su hada wani da Allah ba, ba za su yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe `ya'yansu ba, ba za su zo da wata karya wadda za su kage ta da tsakanin hannayensu ko da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin abin sarari na shari'a ba; to sai ka yi mubaya'a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jin kai". Surar Mumtahanati, 60:12.

Wani aikatau ne kuma dalili na Alkur'ani da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa, a kan kar6ar bai'ar mace ga Maji6incin AI'amari; kai! wajibcin haka ma, domin mubaya'a a wannan aya ita ce bai'ar biyayya ga Majibincin Al'amari, a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari'a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya'a kuwa tana misalta mafi girman ma'anonin hakkokin siyasa a cikin al'ummar dan Adam.

Watakila daga cikin mafi bayyanar dalili a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci, akwai abin da ya zo cikin ayar `Horo da aikin kirkidahanidamummuna', da ayoyin Wilaya da gamammen shugabanci wadanda suka hada maza da mata.

Hakika babban malamin furu'a nan, gawurataccen manazarcin Musulmi Shahid Sayyid Bakir Sadar (r.a) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa Mumini da Mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne; ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa:­

"AI'umma na taka rawarta wajen Khalifanci a tsaikon shari'a, da dalilin ka'idoji biyu na AIKur'ani masu zuwa: 'AI'amurransu shawara ne tsakaninsu' da `Muminai maza da muminai mata kuwa, majibinta al'amarin juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...' Domin nassi na tarko yana ba al'umma damar aiwatar da al'amurranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya sa6a da haka ba. Nassi nabiyu kuwa yana magana ne a kan ji6intar al'amari; da cewa kowane mumini majibincin al'amarin saura ne, saboda dalilin horo da aiki da alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi zahiri ne a kan gudanar wannan jibintar al'amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida. Daga nan za a iya fitar da ka'idar shawara da bin ra'ayin mafi yawa a yayin sabani. "[20]

Hakika mace Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.), kamar yadda ayar Bai'a ta tabbatar da haka; hakika sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa. Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra'ayinta game da Imamancin siyasa da Khalifanci bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w.a.); mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu `yar Manzon Allah Muhammadu (s.a.w.a.) kuma matar Imam Aliyu dan Abi dalibi (a.s.), wadda ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa; har wasu taro mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita; wannan ne ma ya samar da wannan kungiya ta akida da siyasa mai hamayya da bai'ar Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya'a ga Aliyu (a.s.). Hakika ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya'a ga Aliyu (a.s.) alhali tana mai hamayya da bai'ar Sakifa.

Ya zo cikin wasu hanyoyin tarihi cewa:­

"Sai Aliyu ya fita yana dauke da Fadimatu 'yar Manzon Allah (s.a.w.a.) a kan dabba da daddare zuwa mazaunan Ansar, tana neman taimakonsu; su kuwa sun kasance suna cewa: Ya 'yar Manzon Allah, hafcika bai'armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba".[21]

Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadimatu (a.s.) da Khalifa Abubakar (r.a.) da Umar bin Khaddabi (r.a.). Ta hanyar lura da ayoyin nanbiyu (ayar Shawara da ayar Wilayar Muminai), kamar yadda bayanin fassarar su ya bayyana daga Sayyid Sadar, za mu same su a matsayin asasi na tunani mai fadi kan hakkokin siyasa; kai! wajiban siyasa ga al'umma da dukkan mutanenta maza da mata daidai wa daida.

Wata aya kuma wadda ke wajabta aikin siyasa da wajibcin Kifa'i a kan maza da mata, kamar yin tawaye wa mahukunta masu dagawa, tsayar da daular Musulunci, wayar da kan mutane ta fuskar siyasa da wasun wadannan, ita ce fadar Allah Madaukaki:­



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next