Gudummawar Mace



Hakika shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki, ta kuma karakwadaitarwa a kan shi da abin da ba ya bukatar kari a cikin nassosi da karantarwa da matsayi na aikace. Daga cikin su akwai fadar Allah Madaukaki:­

" (Allah) Shi ne Wanda Ya sanya kasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sassanta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma makoma zuwa gare Shi ne (kawai)". Surar Mulki, 67:15.

Haka nan akwai fadarSa Madaukaki:­

"Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu cikin kasa ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa tsammaninku ku rabauta". Surar .Tuma'ati, 62:10

 Haka nan akwai fadarSa:­

"Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kuma kar ka manta da rabonka na duniya..". Surar Kasasi, 28:77.

Kamar yadda shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki da neman kudi, haka ta yi bayani a kan bambamce-bambamcen karfi da iyawar dan Adam, da wajibcin samun kamala ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaikun nau'in dan Adam; Allah Madaukaki Ya ce:­

"...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hldima." Surar Zukhrufi, 43:32.

 Kamar yadda AIkur'ani ya kwadaitar a kan yin aiki,neman abinci da musayar amfanoni; Manzon Allah (s.a.w.a.) na daukar yin aiki da neman arziki a matsayin jihadi da ibada; hakika haka ya zo cikin abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a.) cewa:­

"Mai wahalar neman kudi don iyali kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah".[18]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next