Gudummawar Mace



"Wani rahoto da kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya kawo ya bayyana cewa: kashi 70 bisa dari na mutane biliyan 1.3 da ke raye a cikin halin mugun talauci a duniya su ne mata, kuma akwai kimanin mata biliyan 2.3 da ba su iya karatu da rubutu ba a duniya. Haka nan kashi uku bisa hudu na daukacin matan kasashen Norway, Amirka, Holland da Newzaland na fuskantar hare-haren fyade. AAmirka kuwa, cikin kowadanne dakikoRi 8 mace daya na fuskantar mummunar mu'amala; haka cikin kowadanne dakikolti 6 ana sace mace daya"[8]

Rahoton ya kara da cewa:­ Kimanin mata rabin miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara saboda ciki da suka dauka da cutukan shi, kuma kimanin kashi 40 bisa dari na wannan adadi yan mata matasa ne. Kuma albashin mata miliyan 828 da ke aiki a fagagen tattalin arziki ya fcaranta daga albashin maza da abin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 bisa dari, kuma irin dan tagazawar nan na bankuna da ake ba ma'aikata a duniya ba sa samun fiye da kashi 10 bisa dari na wadannan agaje-agaje".[9]

Haka nan ya zo cikin wani rahoton cewa:­

"A bisa wani bincike da ma'aikatar adalci ta kasar Amirka ta aiwatar, an gano cewa adadin sace mutane ko yunkurin sace mata na faruwa a Amirka har sau 310 a kowace shekara, wannan kuwa ya ninka alkaluman da hukumar 'yan sandan cikin Amirka ta F.B.I. ta bayar."[10]

Kuma kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga Washigton ya bayar, a kowace shekara akwai halin yi wa mata fyade har sau rabin miliyan a Amirka; alhali kuwa hukumar 'yan sanda ba ta bayar da sanarwar adadin samuwar sace (mata) ko yunkurin sace su a Amirka ba face dubu 140, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar F.B.I. ya bayyana.

Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar kasar Iran mai suna lddila'at ta bayar a adadinta na 20,401 daga kamfanin dillancin labaran Iran da ke birnin Rom na kasar Italiya, cewa:­ "Matsalar halayyar rashin tausayi na kara matufcar tsananta a tsakanin iyalan Italiyawa, domin halin kashe iyaye a hannun `ya'ya da kashe 'ya`ya a hannun iyaye ya karu fiye da yadda ya kasance a da can. Haka wata jaridar Kasar Italiya, a adadinta na baya-bayan nan, ta dauko wani rahoton Kididdigar shekara-shekara na kungiyar Eruospas cewa: cikin watanni goman farkon na shekara ta 1994, an rubuta halin rashin tausayi har 192 a cikin iyalan Rasar Italiya, wadanda 129 daga wannan adadi suka Kare da kisa. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, irin wannan nau'i narashin tausayi a shekara ta 1993 adadin shi ya kai 112, wanda kusan wannan adadin ya kare da halin kashe-kashe.

wani abu, da ya zama dole a nuna shi ne cewa kimanin kashi 40 bisa dari na laifuffukan iyali ya faru ne a arewacin Italiya, kuma kashi 40.8 bisa dari daga cikinsu sun faru ne a kudancin kasar, alhali kashi 16.1 bisa dari ya faru a tsakiyar kasar. Kuma mafi yawan kashe-kashen iyali da aka yi a shekara ta 1994 sun faru ne a lardin Lombardi da ke arewacin Italiya".

Haka nan jaridar 'Jumhuri Islami', a adadinta na 4,485, fitowarta shekara ta 1994, ta bayar da rohoton cewa:­'MujallarEpidemiology (ilimin annoba) da ke Karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO), a adadinta na 11, na shekara ta 1993 ta rubuta alkaluman Kididdiga na karshe da ya Kunshi adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki (AIDS) a duniya baki daya, inda aka rarraba alkaluman daidai da yankunan duniya dabam-dabam. Alkaluman na nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki da suka tabbata ga wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993, ya kai kimanin 718,893. Kimanin 371,086 na wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar Kan jiki sun fito ne daga nahiyar Amirka, yayin da kimanin 247,577 suka fito daga nahiyar Afrika, kimanin 92,482 kuwa sun fito ne daga nahiyar Turai, adadin da ya kai 4,188 sun fito ne daga Australiya, 3,561 kuwa daga nahiyar Asiya.

Wan aka bi kasa-Kasa kuwa, Kasar da ta fi kwasan adadi mai yawa ita ce Amirka, wadda ta kwashe adadin wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta kimanin 289,320, sai kuma kasar Tanzaniya da ke biye mata da kimanin 38,719, sai Kasar Birazil mai 36,481, sai Kenya da 31,185, sai Uganda mai 34,611, sai kuma Biritaniya mai 26,955, sai Faransa mai 24,226, sai kuma kasar Zaire mai 21,008, sai Spain mai 18,347, sai Italiya mai 16,860, sai Congo (Brazavill) mai 14,655, daga nan sai sauran kasashe su biyo baya.

Kamar yadda za a iya lura, ba kawai kasar Amirka namatsayi na daya ba ne ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta mai karya garkuwa jiki, a'a har ma akwai sabani mai yawan gaske tsakanin ta da Kasashen da ke biye mata. Kuma idan muka dauki wadannan alkaluma na adadin dari, za mu sami wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta a kasar Amirka sun kai kashi 40 bisa dari na dukkan wadanda suka kamu da ita a kasashen duniya 150, wannan kuwa duk da cewa adadin mazauna Amirka bai wuce kashi 5 bisa dari na dukkan al'ummar duniya ba'.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next