Gudummawar Mace



b-Mace na da hakkoki kamar yadda wajibobi suka hau kanta.

c-Maza ke rike da nauyin shugabanci da daukar dawainiyar gudanar da al'amurran gida.

d-Taimakekeniya cikin sha'anonin rayuwar aure.

e-Yin tsaka-tsaki wajen ciyarwa da kiyaye tattalin iyali. f-Kula da nauyi, wato kulawar miji da nauyin da ya hau kansa game da matarsa da sauran wadanda ke cikin iyali; da kulawar mata da nauyin da ya hau kanta game da mijinta, `ya'yanta da iyalin ta. Domin a kanta nauyin kulawa da gida da `ya'ya, tarayya wajen ba su ingantacciyar tarbiyya da yin mu'amala da su da kauna da tausayi da kulawa.

MACE DA TATTALIN ARZIKIN IYALI

Daga cikin manyan matsalolin da suka addabi al'umma,akwai matsalar kudi da hanyoyin shiga ga mutane; da aunawa tsakanin abin da ke shigowa da wanda ake kashewa; hakan na faruwa a tattalin iyali da zarafinshi na kudi wajen ciyarwa da hada-hadar gida. Barnar abinci, abin sha, kayan kwalliya, sutura, mazauni da sauran hidimomi na daga mafi hadarin matsalolin dan Adam; domin akwai almabazzaranci da kashe kudi ba tare da basira ba da ke gurgunta tattalin arzikin iyali, al'umma da gwamnati, wadanda so tari ba sa dacewa da hanyoyin shigar iyali da abin da yake samu.

Saboda tsara ma'aunin tattalin arzikin al'umma ne Musulunci ya yi kira zuwa ga daidaito wajen ciyarwa, ya kuma haramta barna kamar yadda ya yi hani ga, matsolanci, kwauro da rowa.

Daya daga cikin manyan matsaloli wajen ciyarwa ita ce matsalar biyan bukatun iyali da kasafin sa, wadanda mace ke da babban alhakin da ya hau kanta wajen tsara shi da iyakance dabi'arsa.

Hakika shari'ar Musulunci ta sanya gamammun asasai don tsara ciyarwa daga sakewarsa; kamar yadda ta tsara iyakoki na asasi wajen biyan bukatun iyali da kasafinsa a iyakance; daga irin wannan za mu ambaci abin da Allah Ya siffanta "Bayin Mai rahamaآ° da shi a matsayin wani madaukakin abin koyo wajen tsari da lizimci, wanda kuma ya bayyana mikakken tafarkin wajen ciyarwa irin wanda aka yi kira ga mutane su yi riko da shi, Allah Madaukaki Yana cewa:­

"..Kuma wad'anda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin kwauro, sai dai ya kasance tsaka-tsaki ne". Surar Furkani, 2s:67.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next