Gudummawar Mace



"Ibada kashi bakwai ce, mafificiyarsu neman halaliya". [19]

 Hakika malaman furu'a (fikihu) sun yi kokari mai yawa wajen karance-karance da bin diddigin game da yin aiki da neman abinci, inda suka fitar da hukunce-hukuncen shari'a da matsayinta game da aikin sana'a da hidima, kuma suka kasa su kashi biyar ta fuskar shari'a kamar haka:­

1-Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don samun biyan bukatun rayuwa ga mutum ko ga wanda daukar dawainiyarsa ta zama dole a kan shi, a matsayin wajibi; kai! ta ma wajabta wa wanda ake bi bashi kuma yake da ikon yin aiki da ya yi aiki don biyan bashin da ke kansa.

2-Haka nan Shari'ar Musulunci na daukar yin aiki don yalwatawa cikin ciyarwa, samar da jin dadin rayuwa da ayyukan alheri; a matsayin mustahabbi da take kwadaitar da mutum a kan yin haka.

3-Shari'ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana'anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina da wasun wadannan; kamar yadda ta haramta duk wani aiki da ke ja-gora zuwa aikata haram, ko da kuwa shi a kashin kanshi halal ne.

4-Shari'ar na daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu dabam.

5-Koma bayan abubuwan da muka ambata a sama,

asalin da shari'ar Musulunci ke tabbatarwa game da aiki shi ne halalci; da haka yin aiki don tara dukiya ko kara yin kudi wani al'amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari'a ta halalta.

Yayin nazari da bin diddigin ma'anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba za mu samiabin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji da magana da shi sun zo cikin wasu nassosi.

Ayyukan Matar Aure: Shari'ar Musulunci ta iyakance wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure da abubuwa kamar haka:­



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next