Gudummawar Mace



Wata kila karnonin karshe-karshen nan, saboda jahilcin da ya bayyana cikin wasu garuruwan Musulmi kamar sauran garuruwan duniya, sun shaida wani nau'i na kangiya ga mace daga irin tasirin ta na dabi'a, da hardiya ga tafiyarta na cika; abin da ke sanya tilascin yunkurar wa da tunatar da tunane-tunanen Musulunci da suka ta'allaka da ita, domin kuwa sanya mace a fagen da ya dace da ita cikin rayuwa, yana da babbar gudummawa cikin yunkurin al'umma da bunkasarta.

Babu shakka kan cewa wannan gudummawa ya saba da hakikanin yadda mace ke rayuwa a al'ummun da ke bin abin duniya na zahiri, wandanda suka janye wa mace karamarta da mutuncinta, suka so ta zama na'urar tallace-tallace a kafafan watsa labarai, kuma kayan wasa wadda masu kudi ke amfani da ita bisa son zuciyoyinsu; a karshe sai mace ta rasa matancinta, uwartakarta, daukakar tunaninta da taushin ranta, ba ta girbe komai daga hakan ma face ta'addanci, yin watsi da ita a gefe, yanke kauna, wahalhalu da shigar iyali cikin halin kaico da wastewa.

Binciken da ke hannunka, ya kai mai karatu, wata 'yar sassarfa ce a kan gudummawar mace da ayyukanta cikin al'umma bisa tunanin Musulunci. Muna fatan zai sami lura da muhimmanci daga gare ka.

Dukka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.       

MA'ANAR AL'UMMA

AI'umma: na nufin tawagar nan ta mutane da ta hadu daga daidaiku, wadanda alakokina akida da amfanonin rayuwa iyakantattu suka hada su.

Idan har wannan ne gamammiyar ma'anar al'umma, to al'ummar Musulmi ita ce wannan al'umma wadda ake gina alakokin kuma ake tsara amfanoni a cikinta bisa asasin Musulunci.

Za mu iya ta'arifin al'ummar Musulmi da cewa:

"Taron Jama'ar da a siyasance suke zaune a wani lungu na kasa, wadanda suka yi imani da Musulunci, kuma ake tsayar da alakokinsu da tsarin rayuwarsu a bisa asasin Musulunci".[1]

Don haka al'ummar Musulmi al'umma ce ta akida, wadda ke da abubuwan da suka kebanta da ita da siffofinta da ke bambanta ta da wasunta na daga al'ummu. Ita al'umma ce da ta kebanta da tunane-tunanenta, halayenta, dokokinta, tsarin rayuwarta, dabi'unta da sannanta. Hakika AIkur'ani mai girma ya takaita wadannan siffofi da cewa:­



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next