Gudummawar Mace



4-Amma alakar zamantakewa tsakanin namiji da mace, ita ce alakar kauna kamar yadda AIKur'ni mai girma ya fada: "Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne.."

Alkur'ani na bayar da wannan kyakkyawar sura ta alakar namiji da mace a al'umma da cewa ita ce alakar kauna, wadda ta hada mafi girman so da girmamawa, kalmar (ط§ظ„ظˆظ„ظ‰) da ayar ta yi amfani da ita da larabci, tana nufin: mai taimako, masoyi da aboki,da wannan za mu fahimci kimar managarciyar mace, da ita da namiji daidai ne a wannan bayani na Alkur'ani.

Wani abu na zamantakewa da za a iya ganin shi a duniyarmu ta yau wadda ta kaskantar da kai ga mulkin mallaka, danniya da fin karfin dagutai, shi ne bayyanar danniya, fin karfi da mamaya, tasirin wadannan ya bayyana a cikin mu'amalar zamantakewa da tarbiyya a makarantu da gidaje da alakokin ayyuka da tsare-tsaren zamantakewa ta surori dabam-dabam.

Fakuwar 'yanci, kaskanta mutuntakar wasu da yi musu danniya da rashin mutunta bukatunsu, duk wasu abubuwa ne da ake raye tare da su a cikin duniyarmu ta yanzu; ba a yunkurin hamayya da rashin amincewa sai aiyakokin da ba su dace da wadancan halayya ba.

Abin da ya sami mace a karkashin fitinun wadancan halaye ya fi tsananin kan abin da ya sami namiji, domin hakika kasashenmu sun gaji ci baya na al'adu da tunane-tunane na kauyanci wadanda ta hanyarsu aka yi mu'amala da mace da wulakanci ga mutuntakarta, iyawarta da `yan Adamtakarta; kai! a wasu yanayoyi masu yawa namiji ya yi mu'amala da ita a matsayin wata halitta da ba ta kai matsayin mutum namiji ba, sai wasu tunane-tunane, wadanda suka kawar da mace daga rayuwar zamantakewa na ci gaba, suka taso a tsakanin wasu kauyawa wadanda ke fuskantar fakuwar wayewa da rashin fahimtar Musulunci daga cikin Musulmi, wannan kuwa wani sakamako ne na dabi'a ga yanayin tunani, siyasa da zamantakewar da suka yadu. Sai dai abin mamaki shi ne yadda wasu marubuta da masu kira zuwa ga tunane-tunanen abin duniya na zahiri, ke dangana wa Musulunci, wadannan tunane-tunane da abubuwan da mace ke dandanawa na tauye hakki da ture ta daga fagen zamantakewa.

A karkashin yaduwar yanayin jahilci da ci baya ne Musulumi suka kaskantar da kai ga yakin nan na tunanin abin duniya na zahiri da ya fito daga tafarkokin nan biyu na jahiliyyar gabashi da yammaci; ya zama daga manyan abubuwan da wannan yaki ya sa a gaba, akwai yakar tunane-tunanen Musulunci da mayar da hankali a kan yanayin mace a duniyar Musulmi; sai cibiyoyin al'adu da kafafan watsa labarai da ba na Musulumi ba da jam'iyyun da ba su yi imani da addini ba da masu kira zuwa ga abubuwan zahiri na duniya da kawo sauyi, duk suka himmatu wajen janye mace daga wannan yanayi da take raye a ciki a kasashen da suka ci baya, suka jefa ta a tsaikon sakewa da zubar da kimar mace da yin kasuwanci da al'amarinta na siyasa da wayewa; bayan ta bayyana gare su cewa lalata mace ta hanyar jima'i karkashin ikirarin 'yancin mace da hakkokin mace shi ne kawai hanyar lalata bangaren matasa maza da mata; wannan kuwa saboda mace ita ce tushen rudarwa da tayar da sha'awar jima'i. Hakan yada tunanin sakin akalar jima'i da suka kirkirarwa suna da hakkokin jima'i, yana daga mafi hadarin hanyoyin rushe iyali, watsa 'ya'ya da wargaza alakokin mutuntaka masu karfi da ke tsakanin namiji da mace.

Haka shirin tarbiyya da tanajin mace ke fuskantar fuskoki uku kamar haka:­

1-Fuskar da yanayin kauyanci da al'adun da suka ci baya suka haifar da su:itace fuskar da ta ginu a kan asasan wulakanta mutuntakar mace, murkushe iyawarta da boye gudummawarta na zamantakewa da mutunka da ke kafada-da-kafada da na namiji. Wannan itace fuskar da aka gada daga al'adun da suka samo asali daga jahiltar Musulunci, yanayoyin danniya, fin karfin namiji da ci baya na tunani.

2- Fuskar abin duniya na zahiri: Wadda wayewar duniyanci na yammaci ke kira zuwa gare ta. Wannan itace fuskar da ke kira zuwa ga sakin akalar jima’i, abin da ke haifar da wargajewar iyali da mamayar danniya da zalunci a kan mace amma ta wata hanya a karkashin yekuwar hakkokin mace da hakkokin jima'i da wasun wadannan, wanda ya sanya mace ta zama kan-mai-uwa-da-wabin fyade da cutukan zinace-zinace.

3-Fuskar Musulunci: Ita ce fuskar da ta yi imani da kadaicin nau'in dan Adam, ya kuma tsara alaka tsakanin namiji da mace a kan asasan girmamawa da taimakon juna wajen gina al'umma; da tsara alakar jima'i ba a kan asasin halattar jikin mace da jin dadi da shi (haka nan) ba, ko rushe asasan alakokin iyali, kamar yadda yake faruwa a halin yanzu a kasashen Turai, Amirka, Rasha, Sin, Japan da sauransu na daga kasashen da suka tasirantu da wayewar abin duniya na zahiri ba.maimakon haka, a kan asasin girmama mutuntakar mace da ba ta hakkokinta a matsayinta na mutum da ke da abubuwan da suka kebance ta da hakkoki da abubuwan da hakikaninta suka ginu a kai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next