Gudummawar Mace



 


 

 

 

Hakika AlKur'ani ya zana mana gudummawar mace a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da kiransa, da shigar ta cikin hijira da jihadi, kafada kafada da gudummawar namiji, a lokacin da yake magana game da hijira, mubaya'a, mika wilaya, cancantar lada da babban matsayi, alakar namiji da mace da wasun su, a cikin daruruwan ayoyi na bayanai da maganganunsa a kan wadannan al'amurra, kamar fadarSa Madaukaki:­

"Muminai maza da muminai mata kuwa, masoya juna ne; suna umurni da aikata alheri kuma suna hani da daga mummunan aiki..."Surar Taubati, 9:71.

"Ya Ubangiji, Ka gafarta min ni da mahaifana da kuma wadanda suka shigo gidana suna masu imani, da kuma (sauran) Muminai maza da mata, kuma ka da Ka kari kafirai da komai face

halaka". Surar Nuhu, 71:28. "Ranar da za ka ga Muminai maza da muminai mata haskensu na tafiya a tsakaninsu.." Surar Hadidi, 5'l:l?.

A wadannan ayoyi AIKur'ani ya daga mace zuwa mafi girman matsayi da mutun zai iya kai wa a duniya da lahira, shi yana mu'amala da ita da dan'uwanta namiji daidai wa daida; ita da namiji a fahimtar sakon Musulunci masoya juna ne da soyayya ta akida, suna aikin gyara al'umma, da yaki da barna, laifuka da lalacewa, suna daukar sakon alheri da zaman lafiya da gina fcasa.

A aya ta biyu Annabi Nuhu (a.s.) ya fuskanci Ubangijinsa da addu'a ga Muminai mata kamar yadda ya fuskance Shi da addu'a ga Muminai maza; daga abin da wannan ganawa (da Ubangiji) ta kunsa; asasan karimci, kauna da girmama mace na fitowa, wannan kuwa saboda yin addu'a ga wani dauke da dukkan wadannan ma'anoni.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next