Gudummawar Mace



A wata muhawara da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi da matarsa A'isha (r.a.), a wani martani da ya mayar ga wata maganarta, ya ce:­

"Wallahi Allah bai sauya min ita da wadda ta fi ta ba, ta kasance uwar iyali, mai tarbiyyar gida, ta yi imani da ni lokacin da mutane suka karyata ni, ta taimaka min da dukiyarta lokacin da mutane suka hana ni, kuma an azurta ni da `ya'ya ta hanyarta aka hana ni da wasunta".[12]

A wani lokaci ya kasance yana magana game da ita da cewa:­

"Lalle ni ina son mai son ta".[13]

Kuma kamar yadda ya yi magana a kan matsayinta a ranshi da yunkurin da'awarshi da tafiyar sakonshi, haka nan ya yi magana a kan `yarsa Fadimatu al-Zahara (a.s.), inda ya ce:­

"Fadimatu wata tsoka ce daga gare ni, abin da ke cutar da ita yana cutar da ni. [14]

Haka an taba tambayarsa cewa: Ya manzon Allah, wa ya fi soyuwa gare ka cikin iyalinka? sai ya ce:

"Fadimatu 'yar Muhammadu. [15]

Daga madannan nassosi za mu fahimci matsayin mace da mutuncinta a rayuwar Annabi (s.a.w.a.) da da'awarsa, kuma wannan matsayi na Annabci yana misalta tunanin Musulunci na mafi girman daga matsayin mace na mutuntaka da girmama ta.

Watakila ta hanyar wannan takaitaccen bayani na Alkur'ani da tarihi za mu gane cewa mace a fahimtar AlKur'ani da sakon Allah, ita ce mai renon manyan Annabawa (a.s.), wadda ke dawainyar kare su da lura da su da tsayuwa a gefensu; wannan na bayyana karara a rayuwar Annabi Ibrahim, Musa, Isma'il, Isa da Muhammadu (Amincin Allah ya tabbata gare su baki daya), manyan Annabawa da Manzanni (a.s.), jagororin tunani, kawo gyara da wayarwa a doron kasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next