Tambayoyi da Amsoshi



A: Ittifakin manyan malaman wannan zamani kan halaccin ci gaba da takalidin mamaci ya wadatar wajen ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a) dan haka babu bukatan sai an koma ga wani takamammen mujtahidi.

T29: Mene ne fatawarka kan ci gaba da takalidin mamaci cikin mas'alolin da mukallafi ya yi aiki da su yayin rayuwarsa da kuma wanda bai yi aiki da su ba ?

A: Ci gaba da takalidin mamaci cikin dukkan mas'aloli har ma wanda shi mukallafi bai yi aiki da su ba ya halatta kuma yana isarwa.

T30: Mun kasance masu takalidin Imam khumaini (r.a) kana kuma muka ci gaba da yi masa takalidi bayan rasuwarsa, to yana iya yiyuwa wata mas'ala ta sharia ta bijiro mana musammam ma ga shi muna raye ne a zamanin manyan azzalumam duniya, dan haka sai muka ga yana da muhimmanci mu koma gare ka cikin dukkan mas’alolin sharia, a dalilin haka muke so mu komo gare ka mu yi maka Takalidi, shin za mu iya hakan?

A: Ya halatta muku ku ci gaba da takalidin marigayi Imam (r.a), babu wata bukatan ku canza takalidinku daga gare shi (r.a), to idan har wata bukatan neman hukuncin shari'a kan wasu sababbin mas'aloli ta taso, to kuna iya tuntuBar ofishinmu, Allah ya shiryar da ku zuwa ga yardarsa.

T31: Mene ne abin da ya wajaba kan mat yin takalidi ga wani marja'i yayin da A'alamiyyar wani marja'i ta bayyana masa?

A: Wajibi ne bisa ihtiyat ya koma zuwa ga marja'in da ya gano A'alamiyyarsa cikin mas'alolin da fatawar wannar marja’i nasa suka saba da na shi wannan marja'i Aalam.

T32: A wani hali ne ya halatta ga mukallafl ya canza marja'in da yake masa takalid?

A: Canza takalid yana wajaba ne bisa ihtiyat idan shi marja'i na biyun ya fi na farkon sani, kana fatawarsa cikin mas'ala ta saba wa ta farko, to amma idan dai-dai suke to a bisa Ihtiyat ba ya halatta.

T33: Shin ya halatta komawa zuwa ga wanda ba A'alam ba idan fatawoyin shi marja’i A'alam ba su dace da zamaninsu ba ko kuma aiki da su yana da wahalar gaske?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next