Tambayoyi da AmsoshiA: Wajibi ne yin biyayya ga umamin wali amril muslimin cikin al'amurran da suka game musulmai wanda kare addinin musulunci da musulmai yana daga cikin wadannan lamurra, domin kare su daga kafirai da azzalumai da suka kawo hari ma musulmai. BABIN WILAYATUL FAKIH DA KUMA HUKUNCIN SHUGABA (JAGORA) T42: Shin za'a iya daukar mutumin da bai yarda da' wilayatui fakih na mutlaki ba cewa shi musulmi ne hakika? T43: Shin umarnin waliyul fakih suna wajaba A: A bisa fikihun shia wajibi ne ga kowane musulmi ya yi biyayya ga umarnin da suka fito daga waliyu amril muslimin, da kuma mika wuya ga umami da hane-hanensa hatta ga sauran manyan malamai (maraji'ai) to ina ga masu yi musu takalidi! Mu ba ma ganin biyayya ga wilayatui fakih wani abu ne da yake da bambanci da yin biyayya ga addinin musulunci da kuma jagoranci na Imamai ma’asumai (A.S) T44: Hakika ana amfani da kalmar wilayatul mudlaka (iko na gaba daya) a zamanin Manzon Allah(Sawa) da ma'anar cewa shi Annabi(sawa) idan da zai umarci wani mutum da aikata wani al'amari to wajibi ne ya aikata shi ko da kuwa alamarin yana daga lamurra mafi wahala, kamar da annabi(sawa) zai umurci wani mutum da ya kashe kansa to wajibi ne ya aikata hakan, to tambaya anan ita ce: Shin "wilayatul mudlaka" har yanzu tana nan da wannan ma'ana ?tare da cewa shi annabi (sawa) ya kasance ma'asumi ne, amma a wannan zamani babu wani jagora ma'asumi? A: Abin nufi da "wilayatui mudlaka" ga fakih (mujtahidi) wanda ya cika sharudda shi ne cewa shi addinin musulunci wanda shi ne cikamakin saukakkun addinai wanda kuma zai ci gaba da wanzuwa har zuwa ranar alkiyama addini ne na hukunci da kuma jagorantar al'amurran al'umma, dan haka dole ne alummar musulmai da dukkan bangaronnsu su kasance suna da jagora mai mulkinsu (malami) kuma shugaba wanda zai kare su da addininsu daga abokan gabansu, kana ya kare musu tsarinsu, sannan ya tsayar da adalci a tsakaninsu, ya kuma hana masu karfi su zaiunci masu rauni, ya kuma samar da abubuwan ci gaba na ala’du, siyasa da zamantakewarsu. Watakila wajen gudanar da wannan al'amari ya yi karo da manufofin wasu ko bukatunsu ko burace-buracensu ko amfaninsu ko kuma 'yancin wadansu mutane don haka wajibi ne gajagoran musulmai yayin gudanar da al'amarin jagoranci bisa ga fikihun musulunci da ya dauki matakai da suka dace idan ya ga bukatan hakan. Kana dole ne ya zamanto ikonsa da kuma abin da ya yi nufin zartarwa ya zama shi ke da rinjaye T45: Kamar yadda ci gaba da takalidin mamaci ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi bisa yadda fatawar malamai ya tafi akai, to shin umarni da hukunce -hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen jagoran da ya rasu su ma suna bukatan izinin sabon (rayayyen) jagora kafin su ci gaba da wanzuwa ko kuma a'a?
|