Tambayoyi da AmsoshiT115: Macen da ta samu janaba alhali tana cikin haila shin wajibi ne ta yi wankan janaba bayan ta sami tsarki ko kuma ba wajibi ba ne a gare ta tun da daman ba ta da tsarki? A: Wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba bugu da kari Tl16: A wane irin hali ne za'a iya hukunta ruwan da ya fito wa mutum da cewa maniyyi ne? A: Idan har ya biyo bayan sha'awa, da mutuwar jiki da kuma tunkuda yayin fitowa, to yana da hukuncin maniyyi. T117: A wasu lokuta bayan wanka za'a iya ganin sauran sabulu da ya malale a cikin faratun hannu ko na kafa, wanda ba'a iya ganinsa yayin wankan amma bayan fitowa daga bayan gida sai kaga farin sabulun ya bayyana, to mene ne abin yi? Bisa la'akari da cewa wadansu su kan yi wanka ko alwala tare da cewa sun jahiici hakan ko kuma ma hankalinsu bai kai ga hakan ba, kana tare da cewa ba'a da yakinin cewa ruwa ya ratsa wannan farin? A: Dan kawai kasantuwan fari-fari sabulu wanda ya bayyana bayan gabobin jiki sun bushe bai cutar da ingancin alwala ko wanka, sai idan hakan zai hana tabbatuwan wanke fata. Tl18: Wani ya gaya min cewa: Wajibi ne kafin yin wanka a tsarkake jiki daga najasa, kana kuma ya ce wai tsarkake jiki dai dai lokacin da ake wanka, wato kamar a tsarkake shi daidai lokacin kana cikin wanka daga maniyyi yana bata wanka, to shin wajibi ne sai na sake Sallolin da na yi su a baya dan kuwa ni dama na jahiici wannan lamari. A: Wajibi ne ya zama an raba tsakanin tsarkake jiki da kuma wankan janaba, to amma ba wajibi ba ne a tsarkake dukkan jikin kafin fara wankan, face dai wajibi ne kowace gaba ta zan tana da tsarki yayin wanke ta, dan haka da mutun zai zan gabansa tana da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallarsa duk sun inganta, to amma fa idan da gaba za ta zama ba ta da tsarki kafin wanke ta, to wanka da sallar ba su inganta ba, wajibi ne ya sake su. T1l9: Idan mutum yayin wankan janaba sai ya yi wani abin da ke bata alwala, to shin wajibi ne ya faro wankan daga farko ko kuma ya karasa wanka kana daga baya ya yi alwala? A: Ba wajibi ba ne ya koma ya faro wankan daga farko ba, face dai sai ya karasa wankan, to amma wajibi ne ya yi alwala yayin yin salla ko kuma wani aiki da yake bukatan alwala.
|