Tambayoyi da AmsoshiT120: Idan wanka din daban-daban wajibai ko mustahbbai ko dukkansu suka taru wa mutum, shin wanka guda ya kan wadatar? A: Idan har a cikinsu akwai wankan janaba, kuma ya kuduri niyyar wankan yana wadatarwa daga sauran hakanan wanda ya yi wanka guda daya da niyyar dukkan wanka da ke kansa to ya isar masa T121: Shin wani wanka ba na janaba ba yana wadatarwa daga alwala? A: A'a ba ya wadatarwa. T122: Idan mutum ya san cewa idan har ya sadu da matarsa ba zai sami ruwan wanka ba, ko kuma lokaci ba zai ishe shi ya yi wanka kana ya yi salla ba, to shin ya halatta ya kusanci matar tasa? A: Idan har zai iya yin taimama a wannan hali, to babu wata matsala ga saduwa da matar tasa. T123: Ni dai saurayi ne dan shekara ashirin da biyu, to a kwanan nan sai gashina ya zama yana zuba wanda hakan ya jawo min matsala, to daga baya sai na kuduri aniyar na sa gashin kanti. To abin tambaya a nan shi ne: Mene ne hukuncin wankana idan har wannan gashi zai hana isar ruwa ga wasu bangarori na fatar kaina domin shi wannan gashin za a yi dashensa ne a kaina? A: Idan har wannan gashi da aka dasa ba za, a iya cire shi ba, ko kuma kawar da shi din zai jawo maka cutarwa ko kunci, kana kuma ba za ka iya isar da ruwa zuwa ga fatar kan naka ba, to wankan tare da shi ya inganta. ABIN DA YA WAJABA DANGANE DA WANKAN DA BAI INGANTA BA. TI24: Mutum ne ya samu janaba kana ya yi wanka, to amma wankan nasa bai yi shi dai-dai ba, to mene ne hukuncin sallar da ya yi bayan wankan, tare da cewa ya jahiici hakan?
|