Tambayoyi da Amsoshi



 Bangaren hukunce-hukuncen shari' a.   Ofishin Ayatullah al-uzma Sayyid Aliyu khamene' i (Allah ya kara masa tsawon rai) 

BABIN TAKLID

TAKLID

T1: A, fatawarka, shin aiki da"ihtiyat" shi ya fi ko kuma yin "taqlid"?

A: Kasantuwar aiki da"ihtiyat" ya ta'allaKa ne da sanin wurarensa, kana da kuna sanin yanayin "ihtiyat" din, kuma ba kowa ya san su ba face mutane kadan, bugu da kari kan cewa aiki da "ihtiyat" yana bukatuwa ga sarrafar da lokaci mai yawa, don haka abin da ya fi shi ne yin taklid ga mujtahidin da ya cika sharudcfan taklid.

T2: Nan ba da jimawa ba 'ya ta za ta cika shekarun balaga, inda daga nan wajibi ne gare ta ta zabi marja'in da za ta masa taklid, tattare da cewa gano hakan babbar matsala ce, don haka mene ne ya wajaba a gare mu?

A: Idan har ita da kanta ba ta gano abin da ya wajaba a kanta dangane da wannan al'amari ba, to a nan abin da ya hau kanka dangane da ita shi ne tunatarwa da kuma shiryar da ita.

T3: Wasu mutane wadanda ba sa da cikakkiyar masaniya yayin da muka tambaye su kan cewa ga wani maija'i suke yi wa "taklid", sukan amsa da cewa mu ba mu sani ba, ko kuma su ce muna wa wane (taklidi) ne. "sai dai kuma ba sa ganin cewa dole ne su koma ga risalarsa dan su yi aiki da ita, to anan mene ne hukuncin ayyukansu?

A: Idan har ayyukan nasu sun yi daidai da "ihtiyat" ko kuma da abin da ya dace ko kuma ga fatawar mujtahidin da daman wajibi ne su koma gare shi, to ayyukan sun inganta ni

T4: Wanda ya bar neman ilmin hukunce- hukuncen shari'a wanda suka dame shi shin ya aikata sabo ne ?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next