Tambayoyi da AmsoshiA: Ba kawai ya kebanta da littafin al-kur'ani ba ne, a'a ya hada da kalmomi da ayoyin al-kur'ani ko da kuwa a wani littafi na daban ne, ko cikin jarida, ko mujalla, ko allo ko kuma rubutu a jikin garu da dai sauransu . T96: A jikin wasu kwanuka da farantai da iyalanmu suke cin abinci an rubuta wasu ayoyin al-kur'ani kamar atul kursiyyi, niyyarsu na yin hakan kuwa shi ne neman alheri da kuma albarka, to shin akwai wata matsala cikin yin hakan? A: Babu matsala ga hakan, sai dai wajibi ne a kiyaye kada a taba ayoyin kur'ani ba tare da alwala.ba. T97: Shin wajibi ne ga mutanen da suke rubuta sunayen Allah ko ayoyin kur'ani ko sunayen ma'asumai (a.s) ta hanyar injunan rubutu su kasance cikin alwala yayin rubutun? A: Ba sharadi ba ne a kasance cikin alwala sai dai taba rubutun ba tare da alwala ba ba ya halatta. T98: Mene ne hukuncin amfani da A: Ba matsala wajen bugawa da kuma yada ayoyin kur'ani da sunayen Allah da makamancinsu, sai dai wajibi ne ga wanda suka isa ga hannunsa ya kiyaye hukunce-hukuncen shari'a na rashin wulakanta su da kuma najasta su, da kuma taba su ba tare da alwala ba. T99: Shin ya halatta ga masu sai da kayayyaki da su kunshe abin sayarwarsu da jaridun da suke da sunan Allah ? kana shin ya halatta a taba su ba tare da alwala ba? A: Amfani da wadannan jaridu wajen kunshe abin sayarwa babu matsala a cikinsa idan har ba ganin hakan wulakanta sunayen Allah da ayoyin kur'ani da kuma sunayen imamai (as) da aka rubuta a jiki ne, to amma dai ba ya halatta ga mara alwala ya taba su alhali yana sane da shi. T100: Mene ne hukuncin rubuta sunayen annabawa da kuma ayoyin al-kur'ani a cikin jarida Tare da yiyuwan kona su ko kuma fadawansu kasan kafa?
|