Tambayoyi da AmsoshiT14: Shin takiidin mujtahidi mamaci, ya dogara ne A: Halaccin taklidin mamaci a farkon farawa, ko kuma ci gaba da takalidin mamaci duka ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi A'alam. HANYOYIN TABBATAR DA IJTIHADI DA A’ALAMIYYA DA KUMA GANO FATAWA T15: Shin ya wajaba a gare ni bayan na gano cancantar wani mujtahidi ta hanyar shaidar adilai guda biyu in sake tambayan wasu A: Yana inganta a takaita ga shaidar adilai guda biyu daga cikin ma'abuta sani (Ahlul khibra) T16: Yaya ake zaben marja'i da kuma karban fatawoyinsa? A: Gano ijtihadi ko kuma A'alamiyyar marja'in Taklid dole ne ya zamanto ta hanyar gwani, ko kuma ta hanyar ilimi T17: Na tambayi wasu malamai kan wane ne A'alam sai suka amsa min da cewa yin taklid wa wane (suka ambaci sunansa)yana wadatarwa, to shin yana halatta in dogara ga maganarsu tattare da jahilcina kan A'alamiyyarsa ko kuma zatona ga a alamiyyarsa ko, kuma ya halatta in dogara kan nitsuwa da nake da ita a kan cewa ba shi ba ne A'alam domin kasantuwan wasu mutane da su ma aka ba da irin wannan shaidar dangane da su, da kuma ire- iren wannan halaye? A: Idan har dalili na sharia(shaidar adilai biyu) ya tabbata kan A'alamiyyar mujtahidin da ya cika sharudda, matukar dai ba a sami mai inkarin wannan shaidar ba, to ita wannan shaidar ta zama hujja ta shari'a wanda za a dogara a kan ta kana ba sharadi ba ne a ce sai an sami yakini ko nitsuwa a kan haka, saannan kuma babu bukatar a wannan hali a ce za a binciko wata shaidar da ta saba hakan. AL-UDUL (CANZA TAKLIDI)
|