Tambayoyi da Amsoshi



A: Jinin da mace ta gan shi yayin da take da ciki idan yana da siffofi ko kuma sharuddan haila, to haila ne, in kuwa ba haka ba to istihala ne, idan har istihala mai yawa (kasira) ne ko kuma matsakaici (mutawassida) ne to wajibi ne ta yi wanka.

T134: Macen da ta ke da takamammen al'ada misali kwana bakwai, to sai daga baya ta fara ganin jini har na tsawon kwanaki goma sha biyu saboda amfani da bututun hana ciki, to shin wannan jini da ya karu akan kwanaki bakwai haila ne ko istihala?

A: Idan har jini ya wuce kwanaki goma, to dai-dai kwanakin hailanta shi ne haila sauran kuma istihala ne.

T135/6: Shin macen da ta yi bari ko kuma. mai zubar da ciki, ta zama mace mai jinin haihuwa kuma?

A: Idan har bayan faduwar jaririn-ko da kuwa jini ne ta ga jini to ana daukan ta a matsayin mai haihuwa ne.

HUKUNCE- HUKUNCEN MAMACI

T137: Shin taba kashin da yake da nama a jikinsa da aka cire ko ya fita dagajikin mutum rayayye, yana wajabta wankan taba jikin mamaci?

A: Na'am a wannan yanayi da aka ambata yana wajabta wanka.

T138: Yayin cire hakori ya kan fita tare da wani bangare na dasashin mutum, to shin taba wannan dasashin yana wajabta wankan taba mamaci?

A: A'a ba ya wajabta wankan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next