Tambayoyi da AmsoshiT80: Mutum ne ya yi wankan janaba, to sai bayan awa 3 zuwa 4 ya so ya yi salla to amma bai san cewa shin wankansa ya baci ne ko kuma a'a, to shin akwai matsala idan ya yi alwala dan samun kwanciyar hankali (ihtiyat)? A: A bisa wannan yanayi da ka ambata sake alwala ba wajibi ba ne, to amma yin "ihtiyat" ya halatta. T81: Mene ne hukuncin wata gaba daga cikin gabobin alwala da ta najastu bayan wanke ta amma kafin idar da alwalar? A: Hakan ba ya cutar da ingancin alwala, na'am wajibi ne a tsarkake wannan gabar idan za'a yi salla. T82: Shin kasantuwar digo- digon ruwa akan kafa yana cutarwa yayin shafa? A: Wajibi ne a busar da wurin shafa daga duk wani digo na ruwa kafin yin shafan? T83: Shin shafan kafar dama yana faduwa idan har hannun daman a yanke yake daga asalinsa? A: A'a ba ya faduwa, face dai wajibi ne a yi shafan da hannun hagu. T84: Mene ne hukuncin mutumin da yajahiici karyewar alwalarsa sai bayan ya gama ya fahimci hakan? A: Wajibi ne ya sake alwalar, haka kuma ya sake duk wani aikin da ke bukatar alwala kamar salla da ya yi a baya da wannan alwalar.
|