Musulmi da Kirista



Duk da mun san mahangar Coci kan dan Adam cewa shi sharri ne, kuma wannan sharrin yana tare da shi har ya mutu sakamakon zunubin asalin da babar dan Adam ta sanya babansu ya yi, kuma wannan sharri da ya faro daga sakamakon zunubin asali ba ya kawuwa sai da fansar jinin Isa (a.s), sai dai duk da haka ba mu samu cikin akidun Kiristanci ba cewa ya halatta zubar da jinin mutane haka kawai. Mahangar musulunci tana ganin asalin mutum alheri ne, sai dai yana gurbata ne idan ya cakuda da wasu tunani munana na al'adu ko karkatattun addinai[3], ko munanan ayyukan lalacewar halaye, don haka ne ma takensa na farko ya kasance shi ne mutun rahama ne ga junansa, kuma ta mahangar da Allah yake so ya kalli dan uwansa ne zai kalla.

Idan kuwa aka samu wani Kirista yana halatta zubar da jinin wasu addinai balle ma a ce lamarin ya taso daga wani malamin Coci, to abin ya munana matuka, kuma wannan kiristan karya yake yi ba kirista ba ne shi sai dai a suna kawai.

Idan da masu wannan da'awar zasu tabbatar da wannan lamarin da haujja to da zamu dora alhakin abin hannun cocin da take yin haka ne kawai ba dukkan Coci ba, ba kuma dukkan kirista ba!

 

5- Karkatacciyar Akida

Akwai masu ganin cewa karkatacciyar akida ce da take kunshe cikin tarihi mai neman ramuwar gayya na abin da aka yi wa wadanda ba musulmi ba take jawo wadannan rikice-rikice.

Masu wannan mahanga suna ganin cewa a tarihin rayuwar daulolin musulmi da aka yi a wadannan yankunan, an samu zalunci da aka yi wa wadanda ba musulmi ba, don haka ne bayan sun samu ilimi da wayewa sai suke rama abin da aka yi musu! Don haka sai ko da yaushe suke shiri su auka wa musulmi don daukar fansa, su yi kisan kare dangi da ya hada da maza da mata da yara babu wani tausayi!

Sai dai wannan ra'ayin idan mun kaddara cewa haka ne, to yana bukatar tabbatar da zaluncin da aka yi wa wadannan al'ummu da sunan musulunci wannan ke nan. Idan kuma mun kaddara an yi zalunci da sunan musulunci to ya hau kan malamai da sauran masanan musulunci su wayar da kansu kan wasu abubuwa kamar haka:

Wannan zaluncin da ake da'awar an yi musu idan haka ne to bai shafe su kawai ba, domin ya hada har da musulmin kansu da aka zalunta a wadannan daulolin, ta yadda ana iya kwace wa musulmi gonarsa, da arzikinsa, ana iya korarsa daga kasarsa.

Wannan zaluncin yana koma wa ga sarkin da ya yi wannan zaluncin ne, wanda shi ne wuka da nama a kan komai don haka ba musulunci ba ne, aiki ne na wasu mutanen daidaiku da suka yi mulki suka wuce.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next