Musulmi da Kirista



Akwai masu da'awar ramuwar gayya a ko da yaushe aka samu rikici, sai dai kana iya rasa ramuwar gayya a kan waye? Kuma me ya yi ake yin ramuwar gayya a kansa? Da sauran tambayoyi da ba su da amsa!. Idan wani ya yi wani abu wanda ba a san shi ba, ba ma'ana a yi ramuwar gayya kan wani, balle kuma shi kansa abin da aka yi din ba a san shi ba!. Kuma ko da an san wani abu da wani ya yi kan wasu mutane, to ramuwa tana hawa kan shi mai laifin ne ba kan wata al'umma ba! Masu hankali da hangen nesa ne suke iya sanin maboyar makirce-makirce irin wadannan.

Da za a samu kwamitin gaskiya don neman warware matsalolin nan masu cin rai da suke addabar al'umma, mu a shirye muke mu taimaka don samun mafita mai dorewa! Sai dai kash!

Da wannan ne zamu iya sanin kima da girman shahararren malamin nan na Iraki mai daraja Sayyid Sistani yayin da yake cewa da makiyan al'ummar Iraki masu sanya bama-bamai a masallatai da hubbarorin ziyarar 'yan Shi'a yana mai cewa: Da zasu kashe rabin Shi'ar Iraki da ba zai bayar da izinin ramuwa ba. Sayyid Sistani ya san sarai cewa; masu yin wannan aiki karyar sunnanci suke yi domin sunan musulunci ma bai cancance su ba.

Wannan shi ne lamarin gaskiya da marubucin Jaridar nan ta "Akhbarul Arab" ta turanci mai suna malam "Jamal al-Khashakji" ya yi furuci da shi yana mai girgizawa da girmamawa ga Sayyid Sistani wannan hikima da tunani mai zurfi nasa, sai dai amma abin bai yi wa malaman wahabiyawa a Saudiyya dadi ba. Malamin yana cewa: Ya kamata malaman Azhar, da mai fatawar Saudiyya, da Sheikh Kardawi su tafi Najaf domin su sumbanci hannun Sayyid Sistani. Yana cewa; Ku sani da Shi'a sun ga dama su ma zasu iya kashe wadannan masu sanya musu Bam, sai dai Sayydi Sistani ya tsayar da wannan fitina, da fatawar da ya ba wa 'yan Shi'a ta rashin halaccin kashe wani mutum musulmi ko mece ce mazhabarsa.

Na gama wannan rubutu da safiyar ranar da Sadik dan Sheikh Muhammad Nur Das (a.j.k) ya rasu a nan Kano sakamkon wutar lantarki da ta ja shi zuciyata tana zafin bakin cikin munanan halayen da aka sanya kasashenmu ciki, sai da safiyar na yi tafiya zuwa Birnin Tehran don warware wani rashin fahimta, sai dai ina can wurin zaman sai wannan labari mai tsananin daci da bakanta rai ya same ni. Don haka duk wanda ya karanta wannan rubutu nawa ya yi salati ya bayar da ladan ga wannan yaro.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Sunday, February 06, 2011

 



[1] Mabani Takmilatil Minhaj; Sayyid Khu'i: Mas'ala 301

[2] Wasa'ilus Shi'a.

[3] Sahih Muslim 4: 2047, H: 2658.

[4] Alwasa'il: j 19, Babi 4, H: 3.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13