Musulmi da Kirista



Hadin kan Musulmi da Kirista

Rikicin Jos (Jos Crises)

 Rikin Jos (Jos Crises) wasu tattararrun fadace-fadace da fitinu da suke kunshe da kyamar juna da kai hari kan juna tsakanin mutanen wannan yankin da suka hada da kabilu mabambanta da masu addinai daban-daban musamman musulunci da kiristanci wanda yakan kai ga rasa dukiya da rayuka. Kuma wadannan rikice-rikice sun fara kafin goman karshe na wadannan shekarun.

Mutum halitta ce mai kima da daraja wurin Allah, kuma Allah ya halicce shi ne domin ya samu kamalar da ta fi ta kowace halitta tun daga aljanu da mala'iku zuwa Ruhu mai girma har ya wuce hakan. Sai dai yana iya yin kasa har ya kai ga mafi munin halitta, sai ya zama kamar kura mai farautar dan'uwansa mutum, ya zama guba mai daci gare shi, ya kasance sharri maimakon ya zama alheri. Lallai ne mun halicci mutum a cikin mafi daidaituwar halitta, sannan sai muka mayar da shi mafi kaskanci kaskantattu: Kur'ani; surar Tin; 4-5.

Dalilai masu yawa ne sukan kai ga mutum zama hakan; wani lokaci matsalar tunani ce take samun sa sakamakon jahilci ko gadon wani mummunan tunani na al'ada, ko munanan halaye kamar hassada da kyashi, ko ingizawa daga waninsa, ko kyamar abu maras dalili, ko bangaranci ko kuma huce haushihsa.

Imam Hasan mujtaba jikan manzon rahama Muhammad dan Abdullah (a.s) yana cewa: Mutum makiyin abin da ya jahilta ne. (Gurarul Hikam: 423)

Musulunci addini ne na rahama da sulhu da zaman lafiya, bai yi umarni da wani ya taba wani ba sai idan ya kasance ta fuskacin kariyar kai ne[1], sannan ya shelanta cewa babu wani tilasci a addini (Bakara: 256).

Don haka ne zamu ga dukkan yakokin da manzon rahama (s.a.w) ya yi a rayuwarsa don kare kai ne, bai taba kai hari kan wasu babu dalili mai karfi ba. Don haka an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowane lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.

Musulunci ya sanya rahama da ayyukan tausayi da jin kai su ne kashin bayan asasinsa, kusan talauci ya kawu daga dukkan daula da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya, kuma ya kasance labari a lokacin halifancin Imam Ali dan Abi Dalib.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next