Hakkoki A Musulunci



Duba ka ga me Imam Ali (A.S) yake cewa game da mai tsaron kasa: “Runduna: Ita ce kariyar al’umma da izinin Allah, kuma adon shugabanni, izzar Addini, hanyoyin aminci, al’ummar kasa ba ta tsayuwa daram sai da su”[37]. A wani wurin yana cewa: “Ka sanya wa rundunarka jagora wanda ya fi su nutsuwa da biyayya ga Allah da Manzonsa a ganinka. Wanda ya fi sirri na gari (wato mai dabi’u masu kyau), wanda ya fi su hakuri, da ilimi, da sanin tafiyar da al’amuran al’umma, da rashin saurin fushi, kuma da karbar uzurin mutane. Mai tausayawa talakawa, maras bayar da dama ga masu karfi. Wanda takurawa ba ta harzuka shi, rauni (karayar zuci) ba ya dunkufar da shi[38]. A cikin wannan akwai nuni da cewa: Cin hanci shi ne abin da yake kawo ba wa mai karfi dama ya taka doka. Kuma akwai nuni da cewa: Bin hakkin dan kasa wajibi ne a kan hukuma a ko’ina ne yake, al’amarin da ya yi karanci a kasashenmu ko ma ba a san da shi ba.

Yana daga cikin hakkin dan kasa a samar masa da wurin shakatawa da walwala da wuraren hutawa da na wasanni da shi da iyalinsa da yaransa. Wani abin takaici irin wadannan filayen da ake warewa unguwanni domin wasanni saudayawa maciya amanar al’umma suka sayar da su al’umma tana gani, mafi ban haushi da muni shi ne mafi yawa ba su san ma cewa wannan hakkinsu ba ne.

Hakkokin Mutane Game Da Arzikin Kasa

Haka nan talaka ba ya ganin ma yana da hakki a arzikin kasa, in banda ‘yan kwanakin nan da wasu ‘yan kadan suka san hakan, al’amarin har ya kai ga wasu daga masu tafiyar da al’amarin al’umma suna neman jahiltar hakan. Saudayawa mai mulki ba ya kiyaye hakkin wanda yake mulka game da arziki da albarkatun kasa, idan kuwa ka ce zaka yi magana kan sauran kayan rayuwa a nan kam sai dai ka mutu da bakin ciki. Duba ka ga wutar lantarki, da ruwan famfo, da man fetur da kasar nan take ita ce ta biyar a duniya a yau. Kuma duba ka ga wasu kasashe da mun fi su karfin tattalin arziki amma ba su da wata matsalar irin wadannan abubuwan rayuwa, man fetur kuwa a wajensu kusan mafarki ne wani ya ce ya ga dogon layi ko babu, kuma a gidaje akwai wuyarin na wutar lantarki da fayef na famfo da na Gas, wannan kuwa duk sun yi shi ne cikin shekaru kadan. Kuma mutanensu suna biyan kudi kankani ne domin duk talaka yana iya biyan kudin. Haka ma a gidaje akwai kayan sanyaya gida a lokacin zafi kuma da abin dumama daki lokacin sanyi, amma wadannan abubuwan a kasarmu a gun talaka wani kayan masu jin dadi ne.

Wani abin kunya da dan Nijeriya yake sha a duniya shi ne; ga shi kasar a waje tana da kima saboda suna jin labarin tana da arziki, amma hatta da gasar kwallon kafar da aka yi a kasar sai ana yi ana dauke wuta. Irin wannan al’amarin ya faru wata rana yayin da muka isa tashar jiragen sama ta Kano, ga fankokin kansu suna bayar da zafi ne amma duk wannan bai isa ba sai aka dauke wuta, wani mutum (ba dan Nijeriya ba ne) ina ji ya ce: Kai ka ga Air port sai ka ce kango. Haka nan ake tara wa ‘yan kasar abin kunya a kasashen waje kai ka ce masu mulki ba sa zuwa wasu kasashe suna ganin abin da yake faruwa.

Hakkokin Mutane A Kotuna

Idan kuwa ka waiwaya kotu abin ya yi muni sosai, amma akwai ma’auni na gane kotun zalunci da kotun adalci, Idan ka ga kotu mai kudi da sarki suna jin tsoronta to ana adalci ne kuma ana bin gaskiya ne, amma idan ka ga talaka kawai ne yake tsoron kotu to ka sani ana zalunci ne. Wani lokaci akan ja shari’a da ya kamata a yanke ta a sati ko awowi kadan amma sai ta yi watanni da shekaru har ma mai hakki ya ce ya yafe, ko ya gaji ya bari don kansa. Wani lokaci hakkin yana rutsawa da kudin marayu ne amma sai ka ga kotu ta ajiye a banki tana samun kudin ruwan, wani lokaci ma ba ya isa sai an diba daga hakkin maraya an sa a aljihu. Wani lokaci kuma akan iya mirgide gaskiya ko jifa da hauka ga wani don wani ya kubuta, da haka ne hakkoki masu yawa na mutane suke salwanta.

Hakkin Malami A Kan Dalibi

Malami yana da hakki a kan dalibi, a takaice muna iya cewa: a girmama shi, da sauraronsa idan yana magana, da barinsa ya amsa tambayar da wani ya yi masa, da kaskantar da kai a gare shi, da kare shi daga mai sukansa, da rufa asirinsa ko aibinsa, da yada kyawawansa da alherinsa, kada ka zauna da makiyinsa, kada ka yi gaba da masoyinsa.

Hakkin Dalibi A Kan Malami

Malami ya tausaya wa dalibai kuma ya san cewa su ‘ya’yansa ne don haka yana neman tsiransu ne, kada kuma ya taba yi musu gori ko kausasa musu hali. Kuma ya rika yi musu nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyonsa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimta da kwakwalwarsu, kada ya yi musu rowa ta Ilimi.

Hakkin Mace A Kan Mijinta

Daga cikin hakkin mace a kan mijinta shi ne ya girmamata, kuma ya tausaya mata da tausasawa, ya ciyar da ita, idan ta yi laifi ya yafe mata, kada ya la’ance ta ko ya zage ta ko ya doke ta, kada ya muzanta ta ko ya kunyata ta ko ya daidaita mata asiri.

Haka nan akwai hadisai da dama da suka zo game da falalar mutumen da yake taya matarsa aikin gida, don haka bai kamata ba al’ada ta rinjayi Addini, don wasu sukan ki hakan saboda wani dalili maras ma’ana na al’ada.

Dole ne miji ya yi adalci ga matarsa da tsakanin ‘ya’yansa da matansa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya nuna mata soyayyarsa, kuma ya nuna mata wannan a fili ta yadda zata zama abokiyarsa a komai. Kuma ya rika yi mata maganganu irin na soyayya da nuna kauna ga juna, bai isa ba ya ba ta kudi kawai don yana da shi, wannan ba ya isa ga bukatun mace. Shi ya sa Allah (S.W.T) ya fada a cikin littafinsa cewa: “Ya sanya soyayya (kauna) da tausayi (rahama) a tsakaninku”[39].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next