Hakkoki A Musulunci



Sai ga wasu wadanda suke kiran kansu musulmi ba sa son a bi Allah a kasashenmu na musulmi, suna kokarin ganin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci, sai ga …

Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa ta sama da ta kasa. Rashin saninsa[14] ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa ko a gode masa. Domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, don haka aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (A.S), amma duka an kashe su ne daya bayan daya[15].

Ba kawai sanin Allah (S.W.T) mahalicci ba har ma furu’a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci duk an jahilci da yawansu a yankunanmu da sauran kasashen musulmi.

Amma nau’in matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare ne, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi, su ba su da shi, babban misali muna iya duba al’amura kamar a Ilimin zamantakewar dan Adam, su sun sanya mutum ne a matsayin Ubangijin kansa, shi ne mai sanya doka da shar’antawa a bayan kasa amma a Musulunci ba haka ba ne, wannan yana daga abin da ya nesanta su daga sanin Allah.

Hatta Musulmi Sun Jahilci Addini

Kamar yadda yake game da kuskuren da Turai suka yi na mummunar fahimta da kuma jahiltarsu game da musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta kuma suka jahilce shi. Babban misali a kasashenmu shi ne: Da zaka ambaci kalmar shari’a sai mutane su yi tunanin irin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu.

Misali da zaka tambayi wanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari’a a Arewa me yake nufi da ba shari’a? Zai ce: Ba gutsure hannu da makamantan wannan, haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka kenan idan yana maganar shari’a. wato wannan shi kenan shi ne musulunci.

Saboda haka dole ne a tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunci yana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi, ba kowa ne ya san shi ba don ba gado ba ne kuma ba al’ada ba ce.

Ba A Karanta Akidu Da Tarihi

Babbar matsala a cikin al’ummarmu ita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu’a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (S.W.T). Ash’arawa sukan takaita a kan Littafin Kawa’idi ne da mafi yawa ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al’makalat da Al’ibana na Al’ash’ari shi kansa mai Mazhabar Ash’ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a Mazhaba ko Akida ba.

Haka sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al’amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba Shin ka so ka sani?

Sai na ce da mai wannan tunani: Da bambanci, domin na su baba bai shafi makomarka ta Lahira ba, kuma ba ka son sanin waye Manzo (S.A.W) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Amma na tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (S.A.W) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next