Hakkoki A Musulunci



Bugu da karin cewa, da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar ‘yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar ‘yan’uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma’anar cewa, ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa’ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan’uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.

Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.

Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne; ya kasance yana jin hakkin ‘yan’uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisi mai zuwa.

Saudayawa sha’awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne, ransa ta yarda da adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha’awarsa.

Saboda haka ne ma kiyaye hakkin ‘yan’uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da ‘yan’uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa “Almu’ula Bn Khunais” bayanin tambayarsa game da hakkin ‘yan’uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi a bin da ba zai iya aiki da shi ba.

Sai Mu’ula ya ce[52]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?

Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.

Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?

Sai ya ce: Ya Mu’ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.

Na ce: Babu karfi sai da Allah.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next