Hakkoki A Musulunci



3-Shari’ar Musulunci ta haramta yin ayyukan da aka haramta, kamar sana’anta giya, miyagun kwayoyi, raye-raye, zina, caca, riba, da wasun wadannan, kamar yadda ta haramta duk wani aiki da yake jagora zuwa aikata haram ko da kuwa shi a kansa halal ne.

4-Shari’ar tana daukar wasu ayyuka a matsayin makaruhai a kashin kansu ko saboda wani abu daban, kamar sayar da likkafani.

5-Asalin da shari’ar musulunci take tabbatarwa game da aiki shi ne halacci, don haka yin aiki don tara dukiya ko kara kudi wani al’amari ne na halal matukar yana gudana a kan hanyar da shari’a ta halatta.

Yayin nazari da bin diddigin ma’anonin ayoyi da nassosi, a cikinsu ba zamu sami abin da ya hana mace yin aiki ba, ko ya kebe halaccin haka ga namiji, duk kuwa da cewa kwadaitar da namiji a kan aiki ya zo a cikin wasu nassosi.

Hakkin Yin Aiki Ga Matar Aure

Shari’ar Musulunci ta tanadi wasu hukunce-hukunce da suka kebanci aikin matar aure kamar haka:­

1-Yana daga hakkin mace ta shardanta wa miji cewa ba zai hana ta yin aiki ba a lokacin daura aure.

2-Miji ya amince a kan aikin matarsa ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu, wannan kuwa idan ta so yin aiki ba tare da wani sharadi da ya gabata ba kenan. Idan kuwa miji ya ki amincewa da matarsa ta yi aiki a irin wannan hali, ba yana nufin cewa shari’ar musulunci ce ta hana mace aiki ba.

3-Idan mace ta yi aure alhali ta riga ta yi yarjejeniyar aiki na wani ayyanannen lokaci da wasu to yarjejeniyar aikin ba ta baci ba koda kuwa ya sabawa hakkin miji.

4-Idan matar aure ta kulla yarjejeniyar aiki ba tare da izinin mijinta ba to ingancin wannan yarjejeniya ta dogara ne a kan yardar mijin idan aikin ya sabawa hakkokinsa, idan kuwa bai saba wa hakkokinsa ba, to yarjejeniyar tana zartuwa.

5-Hukuncin duk wata yarjejeniyar aiki da mace ta kulla tana gudana ta hanyar nazarin hukunce-hukuncen shari’a, ba zamu taba samun wani nassi da yake haramta yin aiki ga mace ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next