Hakkoki A Musulunci



Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas’alolin Addini[26] wannan na malamai ne, kamar yadda shehu Usman dan fodiyo (R.A) ya yi nuni da haka yayin da yake nuni da bidi’oin da aka farar cikin Addini da cewa: Shi malami kada ya sa mutane cikin rikicin Addini haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra’ayi kan mas’aloli abu ne na malamai.

Hakkokin Garuruwa Ne A Tsaftace Su

Rashin kula da tsafta daga bangaren gwamnati da kuma al’umma yana daga cikin mummunan al’amari da addabi birane da kauyuka, ta yadda zaka ga duk ko’ina ana iya zuba shara[27]. Ga mummunan tsarin da garuruwa suke fama da shi, sai a sayar da hanyoyi har da hanyar ruwa ta yadda damina da kwararar ruwa zasu wahalar da talaka, ga karancin manyan hanyoyi da matsattsun kananan lunguna[28]. Idan kuwa damina ta zo talakawa suna fargaba ne, ga miyagun lunguna da kududdufai marasa hanya, amma ba za a rushe gidaje a fadada hanyoyin ruwa da na motoci da yin kwatami don samar da magudanar ruwa ba.

Mafi girman abin takaici shi ne abin da na gani a Jami’ar Bayaro da na dade ban ga irinsa ba, sai na ga takardu a ko’ina a kasa, matattakala duk da tabo ta yi bakin kirin, muna tsaye muna hira sai wani ya watso ruwa daga sama duk ya kusa bata mu, idan kuwa ka wuce wasu wurare wari yana tashi. Sai na fara tunanin Jam’iar Tehran da wuri ne kodayaushe kamar ka sanya abincinka a kasa ka ci, na rika tunanin cewa a yanzu da wani zai zo daga abokanmu daga Jami’ar ya ga wurin kwanan dalibai kawai da an ji kunya. Kuma da zaka tambaya a kan me aka gina imani? Daya daga mafi muhimmancinsu ita ce tsafta: Hatta ma wasu hukunce-hukuncen Allah yakan sanya su ne domin kai wa ga cimma samuwar tsafta a cikin al’umma.

Ba ma jami’a ba, a irin wadannan kasashe a cikin gari duk wani yanki a kowane dare yana da motoci na musamman wadanda da dare sukan wanke titinan yankin. Amma wani abin takaici a kasarmu ba ma kawai tsaftar gari ba, kana iya ganin yanki da miliyoyin mutane suke rayuwa ba tare da wani isasshen ruwan sha ba.

Hakkokin Da Suke Tsakanin Mutane

Kowane mutum yana da hakkoki masu yawa a kan dan’uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma’auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: “Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi”[29]. Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.

Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da ‘ya’ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau’i na mutane gaba daya.

Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar duka ko da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare da na Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.

Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izinin uba[30], ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da ya zama sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mai nushuzi[31], shi ma a mataki na uku na karshe[32] kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.

Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.

Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al’umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al’umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next