Hakkoki A Musulunci



Haka nan ba shi da kyau ga miji ya munana zato ga matarsa, ko ba komai munana zato ga musulmi haramun ne, idan mace ta san mijinta yana munana mata zato alhalin tana mai kame kanta wannan yana iya rusa alakar soyayya da girmama juna da ke tsakaninsu har ya kai su ga rabuwa.

Hakkin Miji A Kan Matarsa

Daga cikin hakkin miji a kan matarsa shi ne: Kada ta ki shimfidarsa in ya neme ta, kada ta bayar da izinin shiga gidansa ga wanda ba ya son shigarsu, kada ta yada sirrinsa ko ta yi masa barnar dukiya, ta kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafeta, kada ta kausasa masa harshe, ta yi kokarin faranta masa rai. Sannan ta rika ba shi uzuri a kan wasu al’amuran, kada ta yi abin da zai sa shi ya ji baya son zama da ita a gida ko abin da zai sanya shi nisantar hira da ita ko kaurace mata.

Wasu ruwayoyi sun kawo hakkin miji kan matarsa kamar haka: Yayin da wani sahabi ya ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki sai ta yaye masa shi, idan kuwa ba ya nan tana kare shimfidarsa ba ta ha’intarsa, kuma ta kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar ‘ya’yansa. Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya ba shi amsa da cewa: “Allah yana da ma’aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidi”[40]. Haka nan wata ruwaya ta nuna cewa: “Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah”[41].

 Haka nan dole ne ta yi biyayya a gare shi[42] domin shi shugaba ne a gida babu kuma yadda mutane biyu zasu hadu a wuri ba tare da shugaba ba, ta sani rashin biyayya a gare shi yana rusa masa ruhinsa da karya masa zuciya, sai ya fara tunanin daukar fansa sai gaba ta faru, kuma zamansu ya gurbace, ko kuma wannan fushin ya tura shi ga miyagun halaye da kuma yawan fusata da fada.

Kada wata mata ta rika gasa da wasu mata ta ce: An saya wa kawata kaza kai ma sai ka yi min kaza wannan ko kadan ba shi da kyau. Yana da kyau mata su dauki samfurin rayuwar zamantakewa daga Imam Ali (A.S) da sayyida Zahara (A.S), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (A.S) ya shiga wajan Fadima (A.S) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu sai ta ce: “Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komai”. Sai ya ce: “Me ya sa ba ki gaya min ba” Sai ta ce: “Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shi”.[43]

Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (A.S) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado, kamar yadda maza su kuma su kiyaye ba kwauro ba barna.

Hakkokin Iyaye A Kan ‘Yaya

A nan saboda girma da muhimmancin hakkin iyaye a kan ‘ya’yansu babu wani abu da zamu ce sai dai; duk abin da kasan zaka yi in dai bai saba wa shari’a ba don faranta masu rai to wannan abin ka yi shi, idan kana da da zaka iya gano sirrin haka, duba ka ga danka da wahalar da kake sha a kansa, wannan kuwa bai kebanta da mai da ba domin hankali yana iya fahimtar wahalar rayuwa da iyaye suke sha a kan ‘ya’ya.

Akwai hadisai masu yawa da suka zo game da girmama iyaye da kuma biyayya a gare su kamar haka;

1-Wanda ya yi kallo zuwa ga iyayensa kallo na rahama Allah zai rubuta masa ladan aikin Hajji[44].

2- Wanda ya kalli iyayensa kallo na wulakanci Allah ba zai karbi sallarsa ba koda kuwa sun kasance suna masu zaluntarsa ne[45].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next