Hakkoki A Musulunci



Amma duba Musulunci ka ga ni, koma ka san Allah ka ga tsari da mulki wanda ya shimfida da yadda aka sanya dokoki aka ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi’ar halittar dan Adam, ba bambanci ko fifiko sai da takawa.

Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na Demokradiyya ba, ya zo ne da AsalatusShura[7], Musulunci tsari ne mazhabi[8], amma Demokradiyya tsari ne Ilmi[9].

Daraja Da Sakamako Gwargwadon Sani Ne

Mu sani kamalar hankali yana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu ne. Duba ka gani mana Annabi Nuhu (A.S) duk da ya dade yana shan wahala an ce tun yana shekara arba’in yake kira ga Allah (S.W.T) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, ba domin komai ba sai domin cewa annabi Muhammad (S.A.W) ya fi shi sanin Allah (S.W.T), shi kuma Allah yana sakawa daidai gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari na daga bayinsa.

Wata rana wani Mala’ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawa yana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala’ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala’ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba da yana da jaki da mun kiwata shi. Haka nan Mala’ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: Haka nan abin yake wanda yafi sanin Allah ibadarsa ta rana daya tafi ta jahili na shekaru da yawa.

Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala’ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala’ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala’ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala’ika: Wanene kai? Sai Mala’ika ya ce: Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala’ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta ya ce: Ai wurin yana da aibi. Mala’ika ya ce: Menene aibin? Sai ya ce: Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala’ika ya ce: Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai ya ce: Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala’ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsa ne[10].

Ko mutane haka suke yi a ayyukansu domin a bisa dabi’ar dan Adam ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma sabawa dabi’ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al’amari na saba wa dabi’ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi’ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka.

Misali; A tattalin arziki, lokacin da su Lenin suka so kafa Gurguzu (Kwaminisanci) da suka ga ba zai yiwu ba sai suka kafa Gurguzu mai sauki (Soshiyalizm): A nazarinsu aiki shi ne yake bayar da kima ko mallaka. Saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yake bayar da kima da mallaka. Wannan kuwa al’amari ne da ya saba wa dabi’ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko’ina ba suka rushe. Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al’amarin da su Lenen suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa.

Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, Me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa. Haka nan ne yake wajan Allah tunani da sani su suke bayar da kima ba kawai aiki ba. Amma kada mu manta cewa sanin da ba a aiki da shi mummunan abu ne maras amfani.

Masu Hana Sanin Allah Da Hakkokinsa

Sannan kuma ba a bari Annabawa (A.S) sun kafa Daular Allah ba, kai hatta da lokacin Manzo (S.A.W) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (A.S) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya.

Kasar Farisa ta fi kowace kasa aikata Addinin Musulunci a hukumance da a siyasance, amma su ma ba su kai kashi hamsin cikin dari ba sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (A.S) ne kawai Allah zai ba shi ikon kafa hukuma ta Allah mai aiki da cikakkiyar shari’a[11], shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba[12]. Imam Sadik (A.S) yana cewa: Idan imam Mahadi (A.S) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (A.S), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yi hukunci[13].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next