Hakkoki A Musulunci



Hakkokin Allah Madaukaki A Kanmu[2]

Hakkin Allah (S.W.T) shi ne kadaita shi ba tare da yin shirka da shi ba, kuma da bin umarninsa da nisantar haninsa, da bauta masa ba tare da shirka ba, da yin Salla, da Zakka[3], da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakar da ya gindaya mana. Amma akwai magana kan cewa tun da kadaita Allah ba ya yiwuwa sai da saninsa shin zai yiwu a yi koyi[4] a akida?  wato imani da Allah da kadaita shi ya kasance a bisa dogaro da biyayya ga fatawar malami ko kuwa hakan ba ya inganta?

Sanannen abu shi ne bai halatta ba a dogara da fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi[5], wajibi ne a akida a yi imani da hakan a zuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami. Misali a kan haka; da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma’a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma’a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi sai ya mutu ko kuma ka gano wani wanda ya fi shi ilimi ya ce: Ai Azahar kawai ta isa ko Jumma’a kawai ta isa yaya zaka yi? Amsa ita ce, sai ka koma wa fatawar Malami na biyu domin nan furu’a ce kuma tana kama da aikin likita ne a Asibiti da kake komawa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata.

Amma a Akida da wani malami zai ce da kai: Ai ya gano Allah biyu ne ko sama da hakan yaya zaka yi? Sai ka bi shi? A’a. A nan sai ka ce: Malam nan dai rike Akidarka ko ka kawo wani dalili karbabbe na hankali domin ba a yi wa kowa koyi a kan Akida, haka ma da zai ce: Ya gano shi ya yi ka ba Allah ne ya halicce ka ba.

Hakkokin Allah (S.W.T) a kan ‘yan Adam suna da yawa kuma aiki jajir yana kanmu, sai a mike domin a san su a kuma aikata su. Rashin sanin hakkokin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa daidai take da jahiltar kawuka kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, don haka ne jahiltarsa ta sanya rashin sanin kawukanmu[6], rashin sanin kawukanmu kuwa ya kai mu ga rashin girmama junanmu. Wannan ne ya sanya ba mai girmama ra’ayin dan’uwansa har a siyasar duniya, duba ka ga yadda aka dauki al’amarin addini kansa cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari’a da zai hana ma’abota mazhabobi mabambanta su yi komai are.

Kuma yana da kyau malamai su kafa wata majalisa da zata hada kowane bangare domin kusanto da ra’ayin juna domin tattaunawa da fahimtar juna don amfanar al’umma gaba daya har ma a koyi yadda ake haura katangun mazhabar juna domin wanda ya ga wata mazhaba a wurinsa ita ta fi sai ya haura ya ketara zuwa gareta. Haka nan ya kamata katangun su zama gajeru daidai yadda za su yi dadin haurawa ga mai son haurawa, kuma wannan shi ne yake iya sanya a san abin da kowa yake a kai da fahimtarsa.

Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yi wa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al’umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. Duba ka ga rikici kan NEPU da NPC da na PRP da NPN da sauransu, har ma cikin Addini kamar sabani da rikicin ‘yan kabalu da ‘yan sadalu wanda har ya kai ga sakin aure, da kuma rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Kuma da zaka tambayi masu rikicin menene ma’anar gaibi da ka samu cewa babu wanda ya sani, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada a kan Bushanci da Sadamanci har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu.

Haka nan a wannan lokaci a kan canja wa wasu rikice-rikicen riga sukan fito da sababbun riguna kamar ba su ba ne, sai dai babu mai iya gane su sai mai idon basira da Ilimi da tunani, misalinsa a yau shi ne batun ‘yan Shi'a da Ahlussunna.

Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, in dai ba neman fitina ba, kasancewar wannan mabiyin Ahlul Bait (A.S) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne ko shafi’iyya ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi bai kamata ba ya cutar ko ya jawo rigima da fitina. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!.

Tsarin Allah Madaukaki

Allah ya saukar da tsarinsa mai cike da hikima wanda ya saba da tsari irin na Kwaminisanci da Demokradiyya, Tsari ne wanda aka jahilce shi a duniya wanda da an san hakikaninsa da hatta wanda ba musulmi ba, ba zai nemi wani tsari ba sai shi. Akwai wasu tsarurruka a Duniya amma ko kadan ba a iya kwatanta su da tsarin Musulunci, Kwaminis ya kafu ne bisa Fomular Hegel da Marks ya dauka ya yi amfani da ita, Hegel ya yi amfani da nazarinsa ne a kafa dalili da ilimin tunanin dan Adam, amma su Marks sun yi amfani da ita a nazari na tarihi ne da kuma juyi na al’umma don neman hada fada tsakanin masu jari da ma’aikata da kuma yakar dabi’ar halittar mutu ta ikon mallaka. Tsari ne mai yakar ‘yan jari-hujja da abokan hamayya, amma ta hanyar zalunci da yakar dabi’ar halittar dan Adam da kisan kare dangi, tsari ne da bai san akwai Allah ba.

Amma Demokradiyya Ita tana dauke da jari-hujja ne da ya  sanya mutum a matasyin Ubangiji da yake da iko sakakke, yana da ikon ya bautar, ya tatse, ya shanye jinin talaka, sannan ya wurgar da kashin, tsari ne mai tsotse talaka har kashinsa ya mayar da shi kamar kwarangwal.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next