Hakkoki A Musulunci



Cikin dukkan wadannan ayoyin ana magana ne ga dukkan musulmi maza da mata, ashe kenan tsayar da Addini da Akidunsa da dukkan tsare-tsarensa na siyasa, zamantakewa, ibada da sauransu, nauyi ne a kan dukkan Musulmi, haka nan umarnin yin biyayya ga majibanta al’amura da ya zo a cikin wannan aya ya doru a kan dukkan baligai, kuma alkawarin mayewa ana fuskantar da shi ne ga dukkan wadanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari maza da mata.

Fadinsa Madaukaki:­â€œYa kai Annabi idan muminai mata suka zo maka suna mubaya’a gareka a kan ba zasu hada wani da Allah ba, ba zasu yi sata ba, ba za su yi zina ba, ba zasu kashe `ya’yansu ba, ba zasu zo da wata karya wadda zasu kage ta tsakanin hannayensu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin wani kyakkyawa ba, to ka yi mubaya’a da su, kuma ka nema musu gafarar Allah, hakika Allah Mai yawan gafara ne Mai jinkai”. Surar Mumtahannati, 60:12.

Wannan wani abu ne da ya faru a aikace, kuma dalili ne na Kur’ani da Manzon Allah (S.A.W) ya aikata shi cikin rayuwarsa ta isar da sako da siyasa game da karbar bai’ar mace, kuma mubaya’a a wannan aya tana nufin biyayya ga majibancin al’amari a kan lizimtar hukunce-hukuncen shari’a da dokokinta, da ikrari da shugabancinsa. Mubaya’a kuwa ita ce mafi girman hakkokin siyasa a cikin al’umma, kuma wannan dalili ne a kan gudummawar mace ta siyasa da hakkokinta na siyasa a Musulunci.

AyatulLahi Shahid Sayyid Bakir Sadar (R.A) ya kafa dalili da wannan aya a kan cewa mumini da mumina sun cancanci shugabancin siyasa, da cewa namiji da mace a kan wannan daya ne. Ya zo cikin nassin abin da ya fada cewa: “AI’umma tana taka rawarta wajen halifanci a tsayar da shari’a, da dalilin ka’idoji biyu na Kur’ani masu zuwa: “AI’amuransu shawara ne tsakaninsu” Surar shura: 38.  da ayar “Muminai maza da muminai mata kuwa, majibanta al’amarin juna ne, suna umurni da aikata alheri kuma suna hani daga mummunan aiki...’ Surar Tauba: 71.

Nassi na farko yana ba wa al’umma damar aiwatar da al’amuranta ta hanyar shawara ne matukar wani nassi na musamman bai zo da abin da ya saba da haka ba.

Nassi na biyu kuwa yana magana ne a kan jibintar al’amari da cewa kowane mumini majibancin al’amarin saura ne, saboda dalilin horo da aikin alheri da hani da mummuna da ya biyo baya. Wannan nassi dalili ne na zahiri a kan gudanar wannan jibantar al’amari tsakanin dukkan muminai maza da muminai mata daidai wa daida.

Daga nan za a iya fitar da ka’idar shawara da bin ra’ayin mafi yawa a yayin sabani.” Musulma ta shiga fagen siyasa a zamanin Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda ayar bai’a ta tabbatar da haka, sun shiga fagen siyasa sun kuma yi tarayya a rayuwar siyasa.

Haka nan mace Musulma ta shiga kuma ta bayyana ra’ayinta game da jagorancin siyasa da halifanci bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W), mafi girman dalili a kan haka shi ne matsayin Fadimatu ‘yar Manzon Allah Muhammadu (S.A.W) kuma matar Imam Aliyyu dan Abi Dalibi (A.S) wacce ta shiga fagen siyasa bayan rasuwar mahaifinta, ta kasance a gefen Aliyyu cikin harkokinta da matsayinta na siyasa har wasu taron mutane daga Muhajirai da Ansar suka hadu tare da ita. Wannan ne ma ya samar da bangaren siyasa mai hamayya da bai’ar Halifa na farko ta Sakifa, kuma mai kira zuwa ga sake yin mubaya’a ga Imam Ali (A.S).

Ta kasance tana ganawa da Ansar (mutanen Madina) a gidajensu tana neman su da su yi mubaya’a ga Imam Ali (A.S), tana mai hamayya da bai’ar Sakifa. Ya zo a cikin tarihi cewa; Sai Aliyyu ya fita yana dauke da Fadima ‘yar Manzon Allah (S.A.W) a kan dabba da daddare zuwa Ansar tana neman taimakonsu, su kuwa sun kasance suna cewa: Ya ‘yar Manzon Allah hakika bai’armu ta gudana a kan wannan mutum, da mijinki kuma dan baffanki ya riga zuwa wurinmu kafin Abubakar da ba mu kauce daga gare shi ba.

Haka nan tarihi ya rubuta muhawarori da matsayin siyasa na hamayya da ya gudana tsakanin Fadima da halifa Abubakar da Umar Dan Khaddabi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next