Hakkoki A Musulunci



Masu haramta aikin mace suna bayar da dalili ne da kasancewarsa a wajen gida wanda fita yana bukatar izinin mijinta, wasu kuwa ba su amince da aikin mace cikin ma’aikatun da ake cakuda maza da mata ba saboda hakan yana haifar da fasadi da fadawa cikin abubuwan da aka haramta.

A nan ya kamata mu yi nuni da cewa aikin da yake haifar da aukawa cikin haram, haram ne ga dukkan jinsosin biyu namiji da mace, don haka matsayi na iya tilasta hana cudanyar da kuma kokarin sanya aiki a hannun jinsin namiji ko mace kamar yadda nau’in aikin yake bukata, ko samar da yanayin da zai hana kai wa ga haram. Sannan mu sani aikata haram ba ya kebanta da yin aiki idan masu aikata haram sun kasance fasikai ne.

Sa’annan ta hanyar wannan aya: “Kuma muka daukaka darajojin sashensu a kan wani sashe don wani sashen ya riki wani mai yi masa hidima..”[64]. muna iya gani cewa; bamabancin iyawa, kwarewa, da karfin aiki, yana sabawa daga wani mutum zuwa wani ba tare da la’akari da kasancewarsa namiji ko mace ba, kuma alkar musayar amfanoni da biyan bukatun rayuwa da hidima suna cika ne tsakanin daidaikun al’umma baki daya. Kuma kowane daya ba tare da la’akari da jinsinsa (namiji ko mace) ba, yana yin kokarinsa da abin da zai iya wajen biyan bukatun al’umma wanda da haka ne shi ma zai sami tashi biyan bukatar. Manomi yana gabatar da kayan noma, injiniya da masanin fanni suna sana’anta na’ura, likita yana bayar da magani, malami yana yin aikinsa na karantar da manyan gobe, dan kasuwa na samar da kayayyakin masarufi a kasuwa, soja yana kare kasa, mai gadi yana maganin barayi, da sauransu.

Darasi da nazarin hukunce-hukuncen Musulunci dukkansu zasu tabbatar mana da cewa musulunci bai haramta wani nau’i na aiki ko ilimi ga mace ba bayan ya halatta shi ga namiji, mace tana iya yin kowane irin aiki kamar noma, sana’a, likitanci, injiniyanci, gudanarwa, ayyukan siyasa, tela, tukin jirgin sama, da sauransu.

A Musulunci babu wani aiki na samar da wani abu ko hidima da aka halatta ga namiji  amma aka haramta shi ga mace, kowa a shari’ar Musulunci daya ne. A kan haka bambancin kawai da yake tsakanin namiji da mace a wasu wajibai ne da aka kallafa wa namiji ko mace, ko wasu maslahohi da suka ginu a kan asasin ilimi da aka yi la’akari da yanayin halittar gabobi ga kowannensu, da kuma wajibcin tsara rayuwar zamantakewa da gudanar da ita.

Asali a shari’ar Musulunci shi ne halaccin aiki, ko wajibcinsa a wasu halaye, in banda abin da shari’a ta haramta, ko abin da yake haifar da fadawa cikin abin da aka haramta. Idan kuwa har akwai wani ra’ayin haramta aiki ga mace daga wajen wasu, to wannan yana bukatar dalili. A tsarin musulunci da abin da ya dora shi a kan musulmi na wajibai aini[65], ko kifa’i[66], ya wajabta su ne a kan maza da mata ba tare da iyakance jinsinsu ba, ya wajabta musu samar da bukatun al’umma gaba daya kamar likitanci, injiniyanci, karantarwa, noma, kasuwanci, sufuri, tsaro da sauransu na daga ayyukan da al’umma suke bukata. Kuma wajibin kifa’i yana iya sauyawa ya zama wajibi Aini a kan mutanen da ikon aiwatar da wannan wajibi ya kebanta da su ba tare da la’akari da jinsin namiji ko mace ba. Sai dai wani lokaci shari’a tana fuskantar da wajabci ga wani jinsi idan aikin ya shafe shi ne kamar aikin likita da ya kebanci haihuwa (unguwar zoma) da al’amuran da suka shafi mata.

Hakkin Harkokin Siyasa Ga Mace

Daga cikin al’amura na asasi da aka sanya a teburin tattaunawa da muhawara na tunani da wayewa a karni na ishirin akwai al’amarin hakkokin mace, daga ciki kuwa har da shigarta cikin harkokin siyasa, abin da yake bayar da mamaki shi ne, cewa wadannan masu kira ga hakkokin mace na siyasa suna fuskantar da tuhumarsu ga tunanin musulunci da akidunsa, suna siffanta su da cewa akidu ne da suka haramta wa mace shiga cikin rayuwar siyasa, kuma suke hana ta aiwatar da ayyukan siyasa. Suna dogara da yanayin zamantakewa da siyasa wadanda suke gani a garuruwan musulmi ba tare da sun tantance musulunci a matsayinsa na tsarin shari’a da dokoki ba, da kuma masu bin musulunci da suka cakuda shi da al’adunsu a a siyasa da zamantakewa[67] ba.

Sun dauka abin da suke gani a kasashen musulmi shi ne ainihin musulunci alhalin ya saba wa yadda ya kamata ya kasance cikin al’ummar musulmi. Domin mace a wadannan kasashe na musulmi da yadda ake yin mu’amala da ita da kimarta a cikin al’ummar musulmi duk sun doru bisa al’adu ne a zamantakewa, da fagagen aiki, da siyasa, da alakarta tare da namiji.

A musulunci siyasa tana nufin lura da sha’anonin al’umma a dukkan fagagensu na rayuwa da jagorancin tafiyar da su ta hanyar Musulunci. Don haka ita wani nauyi ne na zamantakewa da aka dora wa musulmi baki daya, wannan nauyi an dora shi a kan dukkan musulmi ba tare da la’akari da kasancewarsu maza ko mata ba.

Misalin fadinsa Madaukaki: ­â€œâ€¦ ku tsayar da Addini kuma kada ku rarraba”. Surar Shura, 42:13. Da fadinsa Madaukaki:­ “Allah kuma ya yi wa wadanda suka bayar da gaskiya daga cikinku kuma suka yi aiki na gari alkawarin lallai zai sanya su masu mayewa a bayan kasa, kamar yadda ya sanya wadanda suka gabace su masu mayewa...” Surar Nuri, 24:55. Da fadinsa Madaukaki: ­â€œKu bi Allah kuma ku bi Manzonsa kuma da majibanta al’amuranku (Imamai Ma’asumai)” Surar Nisa’i, 3:59.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 next