Hikimar Ziyarar Kaburbura



4-Bukhari yana rubuta cewa: Wata rana Mnazo ya ga wata mata gefen wani kabari tana kuka, sai ya ce mata “Ki mallaki kanki sannan ki yi hakuri a kan rasa wani naki da kika yiâ€‌.[17]

 Amma bukhari bai ruwaito cigaban wannan hadisi ba, amma Abu Da’ud a cikin sunan dinsa ya cigaba da wannan hadisi ga abin yake kawowa: Wannan mata ba ta gane manzo ba, sai ta kalubalanci manzo ta ce: Me ya dame ka dangane da abin da musibar da ta same ni?

 A wannan lokaci sai wata mata da take gefenta ta ce mata kin gane kuwa wannan kowane ne?, Manzon Allah ne (S.A.W).

A wannan lokaci wannan matar domin ta gyara abin da ta yi wa manzo sai ta tafi gidan manzo ta ce masa: Ya manzon Allah ka yi hakuri ban gane kai ne ba. Sa manzo ya amsa mata da cewa: Hakuri a cikin musibar da ta samu mutum shi ne abin da ya dace.[18]

 Idan da ziyartar kabarin â€کyan uwa ya kasan ce wani aiki ne da ya haramta, maimakon manzo ya yi umarni da yin hakuri, zai ce da ita ne: Ke wannan aiki naki ya haramata a fili. Amma sai ya umurce ta da yin hakuri a kan abin da ya same ta ba wai ta nisanci kabarin ba.

 

Index

Next

Back

Index



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next