Hikimar Ziyarar Kaburbura



Tarihin musulunci yana gaya mana cewa: An haifi manzon musulunci ne a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (A.S) Sannan bayan ya kai shekara 40 da haihuwa aka aiko shi a manzanci. Bayan aiko shi da manzanci ya yi shekara 13 a garin Makka yana isar da wannan sako. Bayan wannan ne tare da umarnin ubangiji ya bar inda aka haife shi zuwa garin Madina, Inda a can ne ya yi shekara 10 yana isar da wannan sako na musulunci kuma ya yi fito na fito da mushrikai makiya musulunci, sakamkon bayar da shahidai da ya yi a wannan hanyar ya samu damar daga tutar musulunci a dukkan yankin kasashen Makka da kewayenta (yanki mai girma daga cikin Jaziratul Arab) A shekara ta 11 bayan hijara ne ya koma zuwa ga rahamar Ubangijinsa. Sannan bayan wafatinsa Sahabbansa suka cigaba da wannan aiki na yada musulunci a sassan duniya daban-daban.

 Wannan kuwa ya shafi rayuwar da kokarin Manzo da iyalansa da da mabiyansa ne (kamar yadda muka fadi cewa shi ne tushen wannan cigaba) Saboda haka dole mu yi kokari wajen kare wannan asali.

Kaburburan Shugabannin Addinin Musulunci Suna Nuna Tarihin Musulunci

 Dole ne mu kula da cewa duk wani abu da zai faru a wani zamani yana kore duk wani shakku ga wadanda suke rayuwa a wannan zamani. Amma tare da gushewar zamani sakamkon ko-in-kula na mutane zai sanya wannan yakini da tabbas da yake ga mutane ya ragu. Ta yadda a hankali zai zama ana shakku da tararrabi a kan faruwar wannan abin, ta yadda wani lokaci ma zai koma kamar wata tatsunniya. Abubuwan da suka faru ga addinan da suka gabata a lokacin da suka faru babu wani shakku ko taraddudi a kan faruwarsu, amma sakamakon rashin kulawa a yau sun zama kamar tatsunniya.

 Maimaita wannan mummunan al’amari dangane da musulunci yana da matsala fiye da yadda ya faru a sauran addinan da suka gabata. Domin kuwa addinin musulunci addini ne wanda har zuwa ranar tashin kiyama dukkan mutane dole ne su yi biyya a gare shi, ta yadda zasu sadu da haske ta hanyar hakan. Mutanen da zasu zo nan gaba kuwa zasu iya biyayya ga wannan addini yayin da suka kasance sun samu yakini dangane da hakikaninsa.

Babu shakka daya daga cikin hanyar kiyaye wannan tabbaci na hakikanin addinin musulunci kuwa shi ne kiyaye abubuwan da suka shafi rayuwar Manzo da sauran shugabannin addinan musulunci.

 Magabatanmu Allah ya rahamshe su, sun yi hidima mai yawa dangane da al’ummar yanzu, ta yadda suka kiyaye mana abubuwan da suka zo tun farkon zuwan musulunci. Sakamakon haka ne kai tsaye muke kiran sauran al’umma zuwa ga wannan addini wanda yake hakikaninsa bai samu wani canji ba, ta yadda muke cewa: Karni goma sha hudu ne da suka gabata shugaban Bani Hashim ya ta shi da manzanci daga Allah ya kuma kira mutane zuwa ga Tauhidi da kaurace wa bautar gumaka da kafirci, bayan Mu’ujizozin da ya zo da su. Sannan ya zo da littafi mai girma wanda ya karya makiyansa da shi. Sannan har zuwa yanzu wannan Mu’ujizata har abada tana nan ba tare da wani canji ba.

 Wanda kafin ya fara bayyana kiransa ya kasance yana tafiya kogon hira domin yin ibada ga Allah madaukaki. Bayan cika shekara arba’in da rayuwarsa ya fara kiransa. Wasu mtane daga cikin mutanen Makka suka yi imani da shi, yayin da wasu mafi yawa suka kaurace masa, har ma suka yi nufin su hallaka shi, amma Allah da ikonsa ya boye shi a wani kogo da ake kira (Thaur) wanda yake kudancin garin Makka, ta yadda ya tsira da makiya. Bayan nan kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, a wannan gari ne mutane Aus da Khazraj (wadanda ake kira da Ansar) suka amsa kiransa suka taimake shi. Manzo a tsawon zamansa a garin Madina ya gwabza yaki mai tsanani tsakaninsa da mushrikai da Yahudawa, Ta wannan hanyar ne ya gabatar da shahidai da dama a tafarkin Allah ta yadda suka ba da jinansu a yakin Uhud, Khaibar da Hunain. Manzo (S.A.W). Ta hanyar aika mabiyansa zuwa sassa daban-daban na wannan nahiya ta kasashen larabawa ya samu damar isar da sakonsa zuwa ko’ina a wannan lokaci. A shekara ta 11 ne bayan hijira ya koma zuwa ga ubangijinsa kuma ya yi umarni da rufe shi a cikin dakinsa. Bayan wafatinsa mabiyansa suka cigaba da hanyar da ya bari, ta yadda ba tare da bata lokaci ba, ya yada wannan addini tare da al’adun da Kur’ani ya zo da su a dukkan sassan duniya.

 Wannan shi ne wani yanki na tarihimmu wanda bayan wucewar karni 14 ake maimaita shi. Saboda haka dole mu yi kokarin wajen kare wannan tarihi na mu da duk abin da ya shafi hakan, ba wai ta hanyar wasu dalilai ba marasa tushe mu ruguza wannan tarihi namu!.

 Kamar yadda ya kasance mu shagala game da kiyaye wadannan kayan tarihi, ta yadda babu bambanci a wurin dangane da samuwarsa da rashinsa duk daya yake, (abin da ma ya fi muni shi ne yadda ake ganin cewa rusa wadannan abubuwa yaki ne da yaduwar shirka) Ta yadda a cikin kankanin lokaci an manta da wasu abubuwa na tarihin musulunci, don ha ka bayan wani lokaci zai yiwu a fara shakku dangane da wasu abubuwa na hakikanin wannan kira da Manzo ya zo da shi. Ta yadda kamar su Salman Rushudi maimakon canza addini sai ya yi kokarin inkarin addinin da tarihinsa baki daya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next