Hikimar Ziyarar Kaburbura



1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta "Kada ku yi tafiya. "

2-Jumla ta biyu kuwa, wadda aka kebance: "Sai masallatai uku".

A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la’akari da ka’idar larabci a nan dole mu kaddara wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka:

1-Mai yiwuwa ka iya cewa "masallaci" ne. (wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku)

2-Mai yiwuwa ana nufin "wuri" ne (kada ka yi tafiya zuwa wani wuri sai masallatai guda uku)

Saboda haka bisa ga tsammani na farko, zai zama ma’anar jumla zai zama haka, wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata.

 Saboda haka idan muka dauki wannan ma’ana zai zama cewa Manzo yana magana ne a kan masallatai, wato don mutum ya yi salla kada ya yi wahala don tafiya kowane masallaci sai masallatai guda uku da aka ambata. Saboda haka a nan ziyarar Manzo ba ta cikin abin da aka hana a cikin wannan hadisi domin ba a kansa ake Magana ba. Sannan dalilin da ya sa aka yi hani tafiya wani masallaci domin yin salla domin sauran masallatai hukunci guda garesu babu wani wanda ya fi wani daraja daga cikinsu, saboda haka yayin da mutum yake da damar yin salla a daya daga cikin masallatai me zai sanya ya sha wahala domin ya tafi waninsa.

Misali kamar idan akwai masallacin jumma’a a wani gari me zai sanya mutum ya tafi wani gari domin ya yi sallar jumma’a a can, domin kuwa ladar da zai samu a wancan masallacin ba ta dara wadda zai samu ba a wannan na garinsu.

Amma dangane da wadancan masallatai uku abin ba haka yake ba, domin salla a cikin daya daga cikinsu ya fi salla a cikin sauran masallatai, saboda haka tare da kula da cewa a cikin wannan hadisi an yi magana ne kawai a kana masallatai, don haka tafiya zuwa wasu wurare bai shafi wannan hani na hadisi ba, saboda haka ba ya magana a kan halasci ko haramcin yin hakan.

Amma idan muka dauki ma’ana ta biyu ma’anar wannan hadisi zata kasance kamar haka: kada ka yi tafiya sai zuwa wurare guda uku (masallatai guda uku da muka ambata).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next