Hikimar Ziyarar Kaburbura



4-Imam Sadik (A.S) yana cewa Manzo. (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyama". [43]

Ruwayoyin da dukkan bagarori guda biyu suka ruwaito ta fuskar ma'ana ba su da bambanci, saboda haka suna karfafa abubuwa guda biyu kamar haka:

A-Duk wanda ya je Makka bai ziyarci Manzo ba, to ya yi wa manzon jafa'i.

B-Duk wanda ya ziyarci Manzo, Manzo zai cece shi a ranar kiyama. Saboda haka don mu takaita wadannan ruwayoyi guda takwas daga Shi’a da Sunna sun wadatar wanda yake son karin bayani sai ya koma zuwa ga littfan da muka ambata.

Tattaunawar Imam Malik Tare Da Mansur Dawaniki

 Kadhi Iyadh ya nakalto tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki kamar haka:

Mansur Dawaniki wanda yake khalifa ne mashahuri na Abbasiyya, wata rana ya shiga haramin Manzo yana magana da karfi.

 Malik a lokacin shi ne Fakih a Madina sai ya juya zuwa ga Mansur ya ce: Ya kai shugaban Muminai, kada ka daga muryarka a cikin wannan masallaci, Allah madaukaki ya koya wa wasu mutane ladabi inda yake cewa: "Kada ku daga muryarku saman muryar Annabi"[44]

 Sannan ya ya bi wasu gungu daga cikin mutane ya ce: Lallai wadanda suke kasa da muryarsu a gaban manzon Allah, su ne wadanda Allah ya jarabba zukatansu da takawa"[45]

 Sannan Allah yana cewa Wasu gungun mutane wadanda suke hayaniya a bayan gidan Manzo suna cewa: Ya Muhammad ka yi sauri ka fito daga cikin gida, Allah yana kaico da halinsu, yan cewa: "Lallai wadanda suke kiranka daga bayan gida mafi yawansu ba su da hankali".[46]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next