Hikimar Ziyarar Kaburbura



A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar "Buyut" yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazanta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su.

Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka, domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.

 Kowa ya san cewa an rufe Manzo (S.A.W) a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau’i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne.

Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (A.S) ita an rufe ta ne a cikin gidanta[69]

 Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (A.S) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin ubangiji a cikinsu. saboda haka wadannan gidaje bisa la’akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya.

A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (A.S) da makarantar Imam Sadik (A.S) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dimbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (S.A.W) ba tare da rusa wadannan wurare ba.

Soyayyar Manzo (S.A.W) Da Iyalansa

Ayoyi da hadisai da dama sun zo domin bayani a kan soyayya ga Manzo da â€کyan gidansa (A.S).

Kur’ani ya nuna mana cewa imanin abin ceta shi ne ya kasance yana tare da wanda yake son Manzo da jihadi a tafarkin Allah fiye da komai a cikin zuciyarsa: "Ka ce idan iyayenku da â€کya’yanku da matanku da â€کyan’uwanku da dukiyoyinku wadda kuka tara, da kasuwanci da kuke tsoran ku fadi a cikinsa, da gidajenku da kuke kaunarsu, idan sun kasance sun fi soyuwa a gareku daga Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah sai ku saurara har al’amarin Allah ya zo, Allah ba ya shiryar da mutane fasikai".[70]

Ayar sama tana magana ne a kan abubuwa guda uku wadanda mafi yawa soyayyar mutum takan ta’allaka da su, wato Iyalai da dukiya da gidaje da saye da sayarwa. Amma mumini na hakika shi ne wanda Allah da mazonsa da jihadi a tafarkin Allah ya fi soyuwa a gare shi fiye da wadancan abubuwa da aka ambata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next