Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Amma a wata aya ana bayani ne a kan soyayyar iyalan gidan Manzo ga abin da take cewa: "Ka ce ban nemi wani abu a kan sakon manzancin da na zo da shi ba a matsayin lada sai soyayya ga iyalan gidana". [71]

 Sannan Manzo yana bayyana wasu abubuwa guda uku wadanda suke nuna dandana zakin imanin mutum, daya daga cikinsu shi ne soyayya ga Allah da shi manzon: Abubuwa guda uku ne duk wanda yake da su to ya dandana zakin imani, daya daga cikinsu kuwa shi ne ya kasance a wajan mutum son Allah da manzonsa ya fi komai a wajensa…

 Ruwayoyi da suka zo dangane da son Manzo da iyalansa sun wuce gaban mu kawo su a cikin wannan littafi, saboda haka a nan zamu takaia da wasu ruwayoyi a matsayin misali dangane da wannan al’amari, muhimmin abu a nan shi ne mu san ta yaya wannan soyayya zata tabbata, domin mutum ya isa zuwa ga wannan hadafi akwai hanyoyi guda biyu:

1-Mutum ta hanyar magana da ayyukansa ya yi koyi da koyarwar Allah da manzonsa, ta yadda zai kasance a rayuwa ya yi kokari ya ga bai kauce wa koyarwarsu ba, domin kuwa idan mutum ya zamana yana tsananin soyayya ga wani ba zai taba saba masa ba. Saboda haka ne ake cewa "soyayya ita ce biyayya". Wato sonka da abu yana lizimta maka da yi masa biyayya.

 Sannan Imam Sadik (A.S) a wasu baituka yana bayyana bambanci tsakanin soyayya ta gaskiya da nuna soyayya da ba ta hakika ba, Inda yake bayani akan cewa:

Kana sabon Allah alhali kana nuna soyayya gare shi,

Wannan ba zai taba yiwuwa ba,

Domin da sonka ya kasance a gaskinya ne, to da ka yi biyayya a gare shi,

Domin kuwa masoyi yana bin abin da abin so yake so. [72]

2-Bayyana soyayya ta hanyoyi daban-daban kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next