Hikimar Ziyarar Kaburbura



2-Kada ya je a kabarinsu, domin yi musu addu’a ko makamancin haka: Kada ka tsaya akan kabarinsa.

 Bangare na biyu na wannan aya yana da muhimmanci na musamman a gare mu, wannan kuwa shi ne, shin tsayuwa a kan kabari yana nufin yayin rufewa ne ko kuwa yana da ma’ana fiye da hakan? Amma masu tafsiri suna karfafa ma’ana ta biyu ne, wanda zamu yi bayani dangane da abin da suke cewa kan hakan.

 Bidhawi yana cewa: Ma’anarsa kada ka tsaya a kan kabarinsu yayin rufewa ko ziyara.[7]

 Shi ma Suyudi a cikin tafsirul jalalaini[8] ya tafi a kan wannan ra’ayi, Sannan Arif Bursi a cikin tafsirin Ruhul Bayan[9] da Alusi Bagadadi a cikin ruhul ma’ani[10] ya kawo wannan.

 Saboda haka Allah madaukaki yana hani ga manzo a kan ya tsaya a kan kabarin munafukai yayin rufewa ne ko kuwa domin ziyara. Wannan yana nuni ne a kan cewa manzo ya kasance yana halartar kabarin muminai yayin rufewa ko kuwa lokacin ziyara, sannan yana yi musu addu’a. Domin kuwa idan ba haka ba, babu ma’ana a yi masa hani a kan wannan al’amari.

 Saboda haka idan haka ne ma’anar wannan jumla zata kasance kamar haka: Har abada kada ka tsaya a kan kabarin Munafukai.

 Sakamakon haka ne zai zamana munafukai sun rasa wannan falala su kuwa muminai suna rabauta daga wannan falala, domin kuwa manzo yana iya halartar kabarin muminai lokacin rufe su ne ko kuwa lokacin ziyara domin ya yi musu addu’a.

Ziyarar Kabari A Cikin Sunnnar Manzo

 Bayan ruwayoyi guda biyu da muka kawo farkon wannan bahasi wadanda suke nuna hikimar ziyara, dole a nan mu kara fadakarwa a kan cewa, manzo da kansa ya kasance yana zuwa makabartar “Bakiyyaâ€‌ domin ziyartar kaburburan musulmi. Sannan tarihi ya tabbatar da hakan kamar haka:

1-Musulim a cikin sahih dinsa yana cewa: An ruwaito daga A’isha cewa duk karshen dare yakan tafi makabarta domin ziyara, duk lokacin da ya shiga wannan wuri yana ce musu:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next